Shugaban INEC ya buƙaci Majalisar Tarayya ta dage kan kwaskwarimar dokar zaɓe

Daga WAKILIN MU

Shugaban Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, ya yi kira ga ‘yan Majalisar Tarayya da su yi aiki ba tare da la’akari da jam’iyyar da kowanne ke wakilta ba wajen yi wa Dokar Zaɓe garambawul wanda zai taimaka wajen inganta yadda ake gudanar da zaɓe a ƙasar nan.

Yakubu ya yi wannan kiran ne a wajen bikin ƙaddamar da kwamitin haɗin gwiwar ƙwararru na yi wa Dokar Zaɓe kwaskwarima wanda aka yi a Abuja a ranar Juma’a.

Kwamitin Haɗin Gwiwar Majalisar Tarayya kan Hukumar Zaɓe da Al’amuran Zaɓe ne ya shirya taron tare da tallafin Cibiyar Tsare-tsare da Aikin Doka, wato Policy and Legal Advocacy Centre (PLAC) da kuma Ofishin Harkokin Ƙasar Wajen Birtaniya da Cigaban Kwamanwal, wato UK Foreign and Commonwealth Development Office (FCDO).
 
Mista Festus Okoye, wato Babban Kwamishinan INEC kuma shugaban kwamitin yaɗa labarai da Wayar da kan masu zaɓe a hukumar, shi ne ya wakilci Mahmood a taron.

Yakubu ya ce garambawul ɗin ya zo a kan kari, kuma abu mafi muhimmanci shi ne lallai a tabbatar da cewa gyare-gyaren sun yi tasiri, kuma an yi su ba tare da kallon kowace jam’iyya ba, sannan a cire duk wata rarrabuwar kai, kuma a kammala su aƙalla daga yanzu zuwa watanni huɗu na farko na shekarar 2021.

Idan an tuna, tun a cikin 2020 ne shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan, ya yi alƙawarin cewa Majalisar Tarayya za ta bada haɗin kai wajen zartar da gyaran Dokar Zaɓe ya zuwa ƙarshen watanni huɗu na farko na shekarar 2021.

Shugaban na INEC ya yi na’am da sabon yunƙurin da kuma sadaukarwar da shugabannin Majalisar Tarayya su ka nuna wajen yi wa tsarin dokokin gudanar da zaɓe kwaskwarima.

Yakubu ya ce sabon hoɓɓasan da majalisar ke yi ya zo a kan kari kuma tilas ne a ci gaba da shi tare da aiwatar da shi a cikin tunanin waiwaye da kuma hanzari.

Ya ce lallai ne a tabbatar da yunƙurin ya tafi bisa hanyar kammaluwar sa, hanzari, saka hannu da tunanin dabaru.

Yakubu ya ce hukumar ta sadaukar da kai sosai ga tabbatuwar aikin garambawul ɗin kuma za ta ci gaba da bada shawarwari da za su taimaka wajen ingantuwar harkokin zaɓe a ƙasar nan.

Ya ƙara da cewa gyara tsarin dokokin zaɓe ba wai zai haifar da sauyi farat ɗaya wajen aikin gudanar da aikin zaɓe ba.

Ya ce: “Tsarin Mulki da kuma Dokar Zaɓe ba su iya yin aiki da kan su, kuma dukkan su su na motsawa ne ta hanyar ayyuka ko rashin ayyukan masu ruwa da tsaki a tsarin zaɓe.”

Wani memba a kwamitin ƙwararrun, Malam Sadiq Mu’azu, ya yi nuni da cewa ɗaya daga cikin alfanun yi wa Dokar Zaɓe gyaran fuska shi ne zai tattaro dukkan gyare-gyaren a cikin kundi guda ɗaya.

Mu’azu ya ce babban burin garambawul ɗin shi ne domin a tabbatar da cewa dukkan jam’iyyun siyasa sun kula da haƙƙin maza da mata tare da kawar da duk wani nau’i na bambanci daga cikin jam’iyyun siyasa.

Ya ce, “Dokar ta buƙaci dukkan jam’iyyun siyasa da su tabbatar da cewa shugabanni mata su ne mata ba maza ba kuma dukkan shugabannin matasa za su kasance ‘yan shekara tsakanin 18 zuwa 45 daga ranar da aka yi zaɓuɓɓukan waɗannan muƙaman.

“Kuma dokar ta na so a ƙara yawan kuɗin da ‘yan takarar zama Shugaban Ƙasa ko Gwamna ko Sanata ko ɗan Majalisar Tarayya za su iya kashewa a kamfen.

Ya ce: “An ƙara kuɗin da ɗan takarar Shugaban Ƙasa zai iya kashewa daga naira biliyan ɗaya zuwa naira biliyan 5, sannan an ƙara na ɗan takarar gwamna daga naira miliyan 200 zuwa naira biliyan 1, sai kuma aka ƙara na ɗan takarar Sanata zuwa miliyan 100, na ɗan Majalisar Wakilai kuma zuwa miliyan 70.”

A nasa jawabin, Shugaban Kwamitin Hukumar Zaɓe a Majalisar Dattawa, Sanata Kabiru Gaya, ya ce idan an zartar da dokar kuma aka amince da ita, to za ta taimaka gaya wajen sauya fasalin siyasar ƙasar nan.

Ya ce: “Ba shakka, yi wa Dokar Zaɓe garambawul zai yi tasiri mai kyau matuƙa a kan hanyoyin gudanar da zaɓe waɗanda sun sha gamuwa da ƙalubale a baya tare da tada muhawarori waɗanda su ka yi barazana ga buƙatar yin zaɓe cikin ‘yanci, adalci da inganci.”

Ya ce an ƙaddamar da Kwamitin Ƙwararru ɗin ne domin a cimma iyakance lokacin da za a amince da dokar ya zuwa ƙarshen kwatar farko ta shekarar 2021.

Shi kuwa Antoni-Janar na Tarayya kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami, alƙawari ya yi na yin aiki tare da kwamitin ƙwararrun domin tabbatar da ba a samu cikas ba wajen samun amincewar shugaban ƙasa ga dokar.

Malami, wanda mai taimaka wa shugaban ƙasa ta musamman kan gyaran fuskar harkokin shari’a da hulɗa da ƙasar waje, Misis Juliet Ibekaku-Nwagwu ta wakilta, ya ce, “Zan ci gaba da aiki kafaɗa da kafaɗa da Majalisar Tarayya don tabbatar da a ƙarshe kwaskwarimar ta samu amincewa kamar yadda aka tsara.

“Na tuna da cewa ba a daɗe da gama zaɓuɓɓukan 2015 ba, Shugaban Ƙasa ya amince da ƙaddamar da kwamitocin gyaran fuskar tsarin mulki da dokokin zaɓe a cikin 2016, kuma mu na ta aiki tare da Majalisar Tarayya kuma mun fito da dokoki huɗu waɗanda Majalisar Zartaswa ta Tarayya ta yarda da su kuma ta aika da su zuwa Majalisar Dokoki.”

A saƙon sa na sa alheri, ahugaban sashen gudanar da mulki na FCDO, Mista Sam Waldock, ya ce ƙasar Birtaniya ta na alfahari da goyon bayan da ta ke ba tsarin mulkin dimokiraɗiyya na Nijeriya.

Ya ce, “A cikin shekaru biyar da su ka gabata, Birtaniya ta kashe sama da fam miliyan 50 a kan tsarin dimokiraɗiyyar Nijeriya kuma ita ce ƙasa mafi girma a Afrika mai bin tafarkin mulkin dimokiraɗiyya kuma ta na cikin manyan membobin Kwamanwal.

“Mu na jinjina wa Majalisar Tarayya a kan aikin ta na yi wa wannan doka garambawul wanda zai taimaka sosai har ma bayan an yi zaɓe.

“Kafa kwamitin ƙwararru da aka yi don a hanzarta aiki a kan wannan doka ya na da matuƙar muhimmanci wajen bada gudunmawa ga tsarin dokokin zaɓe na Nijeriya.”

Shi ma a jawabin sa, Babban Daraktan PLAC, Mista Clement Nwankwo, ya bayyana jin daɗi kan ganin za a zartar da dokar a cikin ƙanƙanen lokaci.

Ya ce, “Sakamakon ganin yadda aka kasa a yunƙurin baya na rattaba hannu kan Dokar Zaɓen a cikin 2018, a bayyane ya ke cewar wannan sadaukarwar ta samu amincewar kowa da kowa daga kowane ɓangare, wanda hakan ya nuna kenan yanzu mun samu sabuwar Dokar Zaɓe.

”Tare da goyon bayan Ofishin Harkokin Ƙasar Wajen Birtaniya da Cigaban Kwamanwal, mun samu nasarar yin haɗin gwiwa da Majalisar Tarayya don ganin an cimma burin da majalisar ta ke so a cimmawa.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *