Shugabancin APC: Gwamnoni sun yi mubaya’a ga ɗan takaran Buhari

Daga BASHIR ISAH

Yayin da ya rage ‘yan kwanaki ga babban taron jam’iyya, Gwamnonin jami’yyar APC sun yi mubaya’a ga ɗan takarar da Shugaba Buhari ke ra’ayin ya zama shugaban APC na ƙasa, wato Sanata Abdullahi Adamu (Turakin Keffi).

Da yake magana da manema labarai jim kaɗan bayan kammala taronsu da Shugaba Buhari ƙarkashin ƙungiyarsu ta Progressive Governors’ Forum a Fadar Shugaban Ƙasa a Abuja, Gwamna jihar Kebbi, Alhaji Bagudu Atiku, ya ce sun cimma daidaiton bambance-bambancen da ke tsakaninsu game da babban taron jam’iyyar da ke gabansu wanda zai gudana Asabar mai zuwa.

Atiku ya tabbatar cewa lallai da farko akwai ‘yan saɓani a tsakaninsu amma bayan zaman da suka yi da Buhari an samu maslaha.

Ya ƙara da cewa Shugaba Buhari ya ji daɗin wannan al’amari yadda gwamnonin suka haɗu tare da cimma matsaya guda inda za su samar da shugabannin da za su ci gaba da jan ragamar jam’iyyarsu nan gaba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *