Sin ta buƙaci a yi watsi da tunani irin na cacar baka game da batun Ukraine

Daga CRI HAUSA

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen ƙasar Sin Wang Wenbin, ya ce Sin na fatan dukkanin sassa masu ruwa da tsaki za su yi watsi da tunani irin na cacar baka, game da taƙaddamar Ukraine, kuma su kafa wani tsarin kiyaye tsaron nahiyar Turai mai daidaito da kuma inganci, ta hanyar komawa tattaunawa da gudanar da shawarwari.

Wang Wenbin, wanda ya bayyana hakan a jiya Juma’ar, ya ce Sin na fatan ganin dukkanin sassa, sun rungumi matakan martaba damuwar junan su ta fuskar tsaro, tare da kaucewa abubuwan da za su iya rura wutar yaƙi.

Fassarawa: Saminu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *