Sojoji sun fatattaki ‘yan ta’adda a Katsina

Daga WAKILINMU

A ci gaba da yaƙi da matsalolin tsaron da suka addabi shiyyar Arewa-maso-yammacin Nijeriya, sojoji sun fatattaki ‘yan ta’adda wanda hakan ya yi ajalin wasu manyan ‘yan ta’addan a jihar Katsina.

Bayanan da MANHAJA ta kalato sun nuna cewa, luguden wutar da jirgin yaƙin sojojin sama (NAF) ya yi a Lahadin da ta gabata a yankin Ilela na jihar Katsina, ya haifar da galaba a kan ‘yan ta’addan yankin tare da yi ajalin da damansu a sansanonin Gwaska Dankarami da Alhaji Abdulkarami, wanda duka su biyun gawurtattu ne.

An gano cewa, ‘yan ta’addan da aka halaka su ke da alhakin kai jerin hare-hare a yankunan ƙananan hukumomin Safana da Ɗan Musa a jihar Katsina.

Jirgin yaƙin ya yi ɓarin wutar ne a kan tsaunukan yankin Ilela, inda ‘yan ta’addan ke ɓoyewa suna aiwatarwa da ta’addancin nasu.

A cewar wata majiyar sirri, “Bayan samun rahoton farmakin da ‘yan ta’addan ke kai wa ƙauyukan ƙaramar hukumar Safana da ƙauyen Ilela inda suka kashe mutane 12 a kwanan nan tare da fatattakar wasu, dakarun sama na Operation Hadarin Daji sun nazarci wurin tare da tsara yadda za su magance matsalar.

“Bayanin da ISR suka samu ya nuna cewa, ‘yan ta’addan suna gudanar da harkokinsu a tsaunukan da ke da nisan kilomita 1.5 daga Kudu-maso-yammacin Ilela da kudancin ƙauyen Rubu. An hango ‘yan ta’addan a kan babura 19 bayan sun kai farmaki ƙauyukan.”

Yayin zantawa da manema labarai ranar Litinin a Sakkwato, Mataimakin Sufeto Janar, Ahmad Zaki, ya bayyana yadda aka kama waɗanda ake zargin da bindiga ƙirar AK-47 guda 32, makamai masu linzami guda 2, alburusai sama da 1,000 da sauransu.