Sudan za ta miƙa tsohon Shugaba Omar al-Bashir da wasu jami’ai ga kotun ICC

Ministar Harkokin Wajen Ƙasar Sudan, Mariam al-Mahdi ta ce Sudan za ta miƙa wa Kotun Manyan laifuka ta Ƙasa da Ƙasa (ICC) wasu tsoffin shugabanninta, ciki har da hamɓararren Shugaban Ƙasa Omar al-Bashir, waɗanda ake nema ruwa a jallo kan laifukan cin zarafin bil-adama da laifukan yaƙi yayin rikicin Darfur,

Mariam ta bayyana hakan ne a ranar Larabar da ta gabata, tare da cewa  “Majalisar Ministocin ƙasar ce ta yanke shawarar miƙa waɗanda ake nema ga kotun hukunta manyan laifuka ta duniya.”

A cewar hukumar Suna, an cimma wannan matsayar ne bayan wani taron tuntuɓa tsakanin ofishin Ma’aikatar Harkokin Wajen Ƙasar da sabon babban mai shigar da ƙara na kotun da ke Hague, Karim Khan, wanda ke ziyartar Khartoum.

Rikicin na Darfur ya ɓarke ne lokacin da ‘yan tawaye daga tsakiyar yankin da al’ummar yankin kudu da hamadar Sahara suka fara tayar da ƙayar baya a 2003, inda suke ƙorafin zalunci daga gwamnatin Larabawa da ta mamaye Khartoum.

Gwamnatin Al-Bashir ta mayar da martani tare da kamfen na hare-haren bama-bamai da hare-hare ta sama daga mayakan da aka fi sani da Janjaweed, waɗanda ake zargi da kisan gilla da fyaɗe. An kashe mutane kusan 300,000 kuma an kori miliyan 2.7 daga gidajensu.

Kotun ta tuhumi al-Bashir da laifukan yaƙi da kisan ƙare dangi bisa zarginsa da kitsa yaƙin kai hare-hare a Darfur.

A bara masu shigar da ƙara na Sudan suka soma nasu binciken kan rikicin na Darfur. Har ila yau, kotun na tuhumar wasu manyan mutane biyu daga mulkin al-Bashir, Abdel-Rahim Muhammad Hussein wanda shi ne Ministan Harkokin Cikin Gida da Tsaro a lokacin rikicin, da kuma Ahmed Haroun, babban hafsan tsaro na wancan lokacin

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *