Sun kashe ɗan majalisar Zamfara sun yi garkuwa da ɗansa

Daga WAKILINMU

Wasu ‘yan bindiga da ake zargin ‘yan fashin daji ne sun kashe ɗan majalisar dokoki na jihar Zamfara mai wakiltar mazaɓar Shinkafi, Hon.Muhmmad Ahmad.

An kashe Ahmad ne ran Talata da daddare a kan hanyarsa ta zuwa Kano bayan ya halarci gangamin karɓar Gwamna Matawalle na jihar Zamfara zuwa APC sakamakon sauya sheƙa da ya yi ya bar PDP.

Daraktan Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a na majalisar, Malam Mustafa Jafaru-Kaura, ya shaida wa manema labarai cewa baya ga halaka ɗan majalisar da ‘yan bindigar suka yi, sun kuma sace ɗansa da direbansa.

Ya ce lamarin ya faru ne a Talatar da ta gabata da daddare a Sheme, jihar Katsina a lokacin da marigayin ke kan hanyarsa ta tafiya Kano don kai ɗansa asibiti. An yi jana’izar marigarin a safiyar Larabar da ta gabata.

Kafin rasuwarsa Ahmad shi ne shugaban Kwamitin Majalisar Dokin Zamfara kan sha’anin kuɗi da kasafi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *