Ta haihu bayan ɗaukar juna-biyu tsawon shekaru 60

Wata mace ’yar shekara 92 da haihuwa, ta kasance ɗauke da ciki har na tsawon shekaru 60 ba tare masaniyar hakan ba. Yadda lamarin ya faru, da cutar da ta hassada wannan al’ajabi an gabatar da shi kamar haka; a bisa ƙa’ida, cikin mace na haihuwa yakan ɗauki tsawon watanni tara (9) ne.

A wasu yanayi, ciki yakan zarta watanni tara, amma baya wuce shekara guda. Amma an samu wata mace wacce ta ɗauki ciki har tsawon shekaru sittin, ba tare da ma tasan da cikin ba.

Huang Yijun, ’yar shekara 92 wacce ke zaune a Kudancin Chana ta ɗauki ciki a shekara ta 1948, shekaru uku bayan gama yaƙin duniya na biyu.

Tunda ba ta da sukuni da za ta iya zuwa gwaji da kiwon lafiya, ba abinda ta taɓuka, musamman ma da ta fahimci lokacin haihuwar ta ya wuce.

Huang, ta yi yaqinin cewar, cikin bazai zauna a jikinta tsawon rayuwar ta ba. Amma kash, haka cikin ya zauna har na tsawon shekaru sittin (60), har zuwa shekara 2008 yayin da likitoci suka fayyace tana ɗauke da ciki shekaru 60.

Huang dai, tana ɗauke da wani yanayi ne da ake kira ‘Lithopaedion’, wanda ake danganta shi da macewar ta yi wacce kuma bata fita daga cikin mahaifa ba, kuma duk tsawon lokaci ta gishirince. Gishirince wa yana nufin, ko sanya wani sashin jiki ya yi tauri ko ƙarfi, ko mai ƙin lanƙwasa, saboda taruwa gishiri.

Yayin da jaririn ya mutu a ciki, Huang ba ta je asibiti domin cire ma ta shi ba. Sai jikin, domin kare kansa daga shigar cutuka, ya rufe tayin da gishiri, kamar dai kifin da aka yi dutsurinsa, ya ɗauki shekaru ba tare da ya ruɓe ba.

Matacciyar tayin da gishiri ya rufe ta, ta kasance ta yi tauri, ta zama kamar ‘jaririn dutse’. Tunda girman tayin bai canja ba, macen za ta riƙa yawonta kamar mai ɗauke da ciki har na tsawon shekaru 60.

Huang ta ɗauki ciki ne tana da shekaru 32, kuma tayin an cire shi yayin da take da shekaru 92.

Lithopaedion, ba yanayi ne sabun ba a wannan zamani, domin akwai na’urorin yin sikanin a ko’ina.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *