Talaka ya san cewa Allah kaɗai gatansa

Manhaja logo

Assalamu alaikum, Jaridar Blueprint Manhaja.

A zahirance, rayuwa tana kyau ne da abubuwa uku. Lafiya, abinci da mazauni. Waɗannan sinadaran da suke inganta rayuwa sun zama watan sallah a wurin talaka. Ba kowa ne yake gani ba.

Lafiya ba ta ishe shi ba, bai da gida, bai da abinci, bai da matsuguni. Wurin kwanan sa shi ne inda ya samu wurin kwanciya ko a ina ne. Idan ana rana a kwanyar kansa zafin zai kare a kansa.

Idan ana ruwa tamkar kifi haka zai zama. Irin waɗannan mutane suna da haƙƙi a wurinmu. Suna da haƙƙi a wurin gwamnati. Ba zaɓin su ba ne su kasance haka, amma zaɓin gwamnati ne ta bar su a haka. Haka kuma zaɓin mu ne mu bar su a haka.

Gwamnati tana da wadataccen arziki da za ta iya shiri na musamman ga irin waɗannan bayin Allah. Amma ko kaɗan hukumomi ba su du ba saboda ta wannan ɓangare hatta masu gidan ma ba su tsira ba. A iya sani na, kusan kowani ɓangare a Nijeriya na fama da ambaliyar ruwa a cikin wannan.

Daga Ni’ima Ammar , 09037353330.