Taron jam’iyyar APC na ƙasa

An ce, sannu ba ta hana zuwa. Mu na fatan yadda jama’a ke dako da burin ganin wannan lokaci na gangamin taron jam’iyya mai mulki APC ya zamo an gudanar da komai lafiya.

Amma kuma kar mu manta a kullum akwai wasu ababe masu darajja shugaba kuma su karo mai tagomashi da ƙwaƙƙwarar ƙauna ga talakawa. Adalci idan ya wanzu mulki zai kyautatu. Amana da gaskaya ga shugaba idan sun bayyana tamkar darussa ne daga shugaba zuwa ga jama’arsa.

Tausayi tare da ungo ta kyautata wa duk waɗannan ne makamashin armashi ga mai mulki domin idan an rasa waɗannan duk wani abu tamkar vata lokaci ne ganin yadda kimar wasu ’yan siyasa sai daɗa wanzuwa ta ke, inda wasu kuwa abin gwara jiya da yau ga talakawa.

Mu na fatan waɗanda duk za su zamo shuwagabanni a samu nagarta da adalci tare da ungu a gudanarwarsu.

Daga Mukhtar Ibrahim Saulawa Katsina. 07066434519, 08080140820

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *