Tinubu ya jefa ‘yan ƙasa cikin ruɗani bayan da ya zaɓi Masari matsayin mataimaki

Daga BASHIR ISAH

Ɗan takarar Shugaban Ƙasa ƙarƙashin Jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya zaɓi Alhaji Kabir Ibrahim Masari daga Katsina a matsayin wanda zai yi masa mataimaki a babban zaɓen 2023.

An ce Tinubu ya miƙa sunan Masari ne a asirce, lamarin da ya jefa da daman ‘yan ƙasa cikin ruɗani.

Da alama dai Tinubu ya yi hakan ne don cimma wa’adin da hukumar zaɓe INEC ta tsayar kan jam’iyyun siyasar Nijeriya su tabbatar da miƙa sunayen mataimakin ‘yan takararsu kafin ƙarewar ranar Juma’ar da ta gabata.

Yayin da wannan lamari ya jefa wasu ‘yan ƙasa cikin ruɗani, wasunsu kuwa na ra’ayin zaɓen Alhaji Masarin ya dace.

Sai dai jaridar Daily Trust ta jiyo cewa, akwai yiwuwar Tinubu ya musanya Masari nan ba da daɗewa ba kasancewar har yanzu yana ci gaba da tuntuɓa game da wanda zai zame masa mataimaki.

Masari haifaffen Katsina ne, kuma ya taɓa riƙe muƙamin Sakataren Walwala na Ƙasa na Jam’iyyar APC a zamanin shugabancin Adams Oshiomhole, daga 2018 zuwa 2020, da sauransu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *