Titi Abubakar ta ƙaryata saƙon da aka danganta ta da shi a soshiyal midiya

Daga WAKILINMU

Maiɗakin Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar, Hajiya Titi Amina Abubakar, ta ƙaryata wani saƙo da aka yi ta yaɗawa a soshiyal midiya wanda ya shafi lissafin wasu ‘yan siyasa a PDP da aka ce daga wajenta saƙon ya fito.

Titi ta musanta fitowar saƙon daga wajenta, inda ta ce “Ba na amfani da shafukan sadarwa na zamani, abin da aka danganta da ni a facebook labarin ƙarya ne.”

Ta ce baya ga ƙaryata batun, haka nan tana shaida wa jama’a ba ta amfani da irin wannan salon wajen tura irin wannan saƙo, kuma ba ta umarci wani mahaluƙi ya yi hakan a madadinta ba.

“Shafin facebook ɗin da aka wallafa labarin ba nawa ba ne, kuma bayan bincike da aka gudanar, an gano cewar an daɗe ana amfani da wannan shafin da sunana.

“Abinda aka wallafa na baya-baya nan a shafin inda aka ce na yi wasu kalamai da suka haddasa ce-ce-ku-ce dangane da siyasar PDP da wasu ‘yan siyasa da ba a ambaci sunan su ba, an kitsa shi ne da gangan domin haddasa fitina da kuma ɓata mini suna,” in ji Titi

Don haka ta yi kira ga al’umma, musamman mambobin jam’iyyar PDP da su yi watsi da wannan saƙo wanda ba shi da tushe balle maka kuma ka iya haddasa rabuwar kai a jam’iyya.