Tsohon ɗan jarida, Bashir Mohammed ya rasu

Daga WAKILINMU

Tsohon ɗan jaridar nan kuma mai fashin baƙi kan al’amuran yau da kullum, Bashir Mohammed Baba ya rasu.

A ranar Asabar Allah Ya yi masa cikawa a wani asibitin Abuja bayan fama sa raunin da ya ji sakamakon hatsarin da ya same shi a ban-ɗaki.

A halin rayuwarsa, marigayin ya kasance ƙwararren ɗan jarida kuma mai sharhi kan al’amura a manyan kafafen yaɗa labarai da suka haɗa da NTA da BBC da VOA da DW da Rediyon Prestige da ke Minna da sauransu.

An jiyo da kuma ganinsa a cikin manyan shirye-shiye a gidajen talabijin da rediyo da daman gaske.

Haka nan, ya kasance Babban Hadimi ƙarƙashin Ambasada Bashir Wali a Ma’aikatar Harkokin Ƙasan Waje.

Majiyarmu ta ce za a yi jana’izar marigayin a ranar Asabar a Wudil, Jihar Kano.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *