Tukwicin N1m ga duk wanda ya taimaka aka damƙe ɗan majalisar Bauchi, Yakubu Shehu – ‘Yan Sanda

Daga BASHIR ISAH

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Bauchi ta ce za ta ba da tukwicin kuɗi Naira miliyan ɗaya ga duk wanda ya taimaka mata wajen damƙe ɗan majalisa mai wakiltar Bauchi a Majalisar Wakilai, Yakubu Shehu, wanda take nema ruwa a jallo.

Wannan na ƙunshe ne cikin jaridar ‘yan sanda ta musamman mai lambar bugu – CB: 2685/Bsx/VOL.T/4s wadda mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Jihar Bauchi, SP Ahmed Wakil, ya raba ranar Talata a Bauchi.

Jaridar ta ce Rundunar ‘Yan Sandan Nijeriya, ƙarƙashin ikon Sufeto-Janar, Usman Baba, ta ayyana ɗan majalisa Yakubu Abdullahi Shehu a matsayin abin nemanta ruwa a jallo.

Ana nemansa ne “dangane da batun haɗin baki wajen aikata laifuka, ƙuntatawa, tada tarzoma da kuma kisan kai.

“‘Yan sanda na neman haɗin kan duk wani da ke da muhimman bayanan da za su taimaka wajen kama shi don gurfanar da shi.

“Wanda duk ya san yana da bayanan da za su taimaka wajen damƙo shi ana inya tuntubar lambar waya kamar haka: 08151849417, ko kuma a kai rahoto ofishin ‘yan sanda mafi kusa,” in ji rundunar.