Wasanni: Dare ya gargaɗi ‘yan wasa su guji yin amfani da muggan ƙwayoyi

Daga BASHIR ISAH

Ministan Wasannin Motsa Jiki, Chief Sunday Dare, ya yi kira ga ‘yan wasa da su guji yin amfani da ƙwayoyin ƙara kuzari da duk wani nau’i na fitina.

Ministan ya yi wannan kira ne yayin rangadin da ya je don duba wuraren wasanni na bikin wasannin motsa jiki na ƙasa (NSF) karo na 20 da ke gudana a Benin, babban birnin jihar Edo.

Dare wanda shi ne ya wakilci Mataimakin Shugaban Ƙasa, Yemi Osinbajo a wajen taron buɗe bikin, ya ce bikin zai taimaka wajen gano ‘yan ƙasa masu fasaha a sha’anin wasannin motsa jiki.

Binciken Manhaja ya gano cewa sama da ‘yan wasa 8000 ne za su fafata a bikin NSF na wannan shekara.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *