Xan wasan Nijeriya a gasar Olympics ta lokacin hunturu ta Beijing

By CRI HAUSA

Bisa labarin da kwamitin gasar wasannin Olympics ta lokacin hunturu ta Beijing ya bayar, an ce, Samuel Uduigowme Ikpefan mai shekaru 30 da haihuwa, ya kammala gasarsa a wasannin Olympics na bana, inda ya samu matsayi na 73, a gasar gudu kan dusar ƙanƙara a daji ta gajeren zango, kuma bai kammala wasanni ba cikin gasar gudu kan dusar ƙanƙara a daji mai nisan kilomita 15. Ikpefan ya zama ɗan wasa daya tak cikin tawagar Nijeriya a gasar ta Olympics na wannan karo, kuma shi ne ɗan wasan dusar ƙanƙara na farko a tarihin Nijeriya.

An haifi Ikpefan a ƙasar Faransa, mahaihiyarsa ’yar kasar Faransa ce, kuma mahaifinsa ɗan Nijeriya ne. Ya fara wasan dusar ƙanƙara tun lokacin yana dan shekaru 6. Saboda bai samu damar shiga ƙungiyar ƙasar Faransa ba, Ikpefan ya yanke shawarar shiga ƙungiyar Nijeriya. A shekarar 2018, bayan da ya samu takardar shiga ƙasar Nijeriya, sai ya nemi iznin shaida da haɗaɗɗen kwamitin kula da wasannin dusar ƙanƙara na ƙasa da ƙasa ya bayar, a ƙarshe dai, ya zama wani ɗan wasan ƙasar Nijeriya a hukumance.

Tawagar ƙasar Nijeriya ta taɓa shiga gasar wasannin Olympics ta lokacin hunturu. A shekarar 2018, a yayin gasar wasannin Olympics ta lokacin sanyi ta Pyeongchang, Moriam Seun Adigun ’yar wasan Nijeriya, kuma ’yar ƙasar Amurka, da abokanta sun kafa ƙungiyar wasannin tseren motar dusar ƙanƙara ta farko ta Afirka a gasar wasannin Olympics.

A gasar Olympics ta Beijing ta bana, ƙasashen Afirka guda 5, ciki har da Kenya, da Nijeriya, da Madagascar, da Morocco, da Eritrea sun shiga gasar, gaba ɗaya, akwai ƙasashe 15 daga nahiyar da suka taɓa shiga gasar wasannin Olympics ta lokacin sanyi. A shekarar 1960, ’yan wasan ƙanƙara guda 5 na Afrika ta Kudu, sun shiga gasar wasannin Olympics, lokacin ne kuma karo na farko da ’yan wasan ƙasashen Afirka suka shiga gasar wasannin Olympics ta lokacin hunturu. A shekarar 1984, ɗan wasan dusar ƙanƙara na Senegal, Lamine Gueye, ya zama ɗan wasa baƙar fata na farko da ya shiga gasar wasannin Olympics ta lokacin hunturu.

Fassarawa: Bako Li