Daga BASHIR ISAH
Ƙabilar Ibo a ƙauyen Alor-Agu da ke yankin Ƙaramar Hukumar Igbo Eze ta Kudu a Jihar Enugu, wanda galibinsu Musulmi ne, sun bi sahun sauran musulmin duniya wajen gabatar da Idin ƙaramar salla a yankinsu.
An ga yadda faifan bidiyon da ke nuni da yadda Musulmin yankin suka gabatar da Sallar Idi ya karaɗe kafafen sadarwa na zamani.
Bidiyon ya ɗauki hankalin masu ta’ammali da kafafen sada zumunta na zamanin ne bayan da wani mai suna Siraj Nwansukka, wanda da alama shi ne ya jagoranci sallar ya wallafa bidiyon sallar da suka gabatar a ranar Juma’a.
An ji shi yana huɗuba ko jawabi da harshen Igbo.
Nwansukka ya nuna an yi bidiyon ne filin Sallar Idi a ƙauyen Alor-Agu da ke yankin Ƙaramar Hukumar Igbo Eze ta Kudu a Jihar Enugu.