Yadda ɗan shekara 18 ya kashe matar aure da taɓarya a Kano

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Rundunar ‘yan sandan Nijeriya reshen Jihar Kano ta kama wani matashi ɗan shekara 18 bisa zarginsa da kashe matar aure a jihar.

A wata sanarwa da mai magana da yawun ‘yan sanda reshen Jihar Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar, lamarin ya faru ne a Ƙaramar Hukumar Kumbotso.

Wanda ake zargi da aikata kisan mai suna Abdulsamad Suleiman, ya amsa laifin ga ‘yan sandan inda ya ce tun da farko ya shiga gidan matar inda ya same ta a kan gado, bayan ya gaishe ta sai ya ga wayoyi uku sa’annan ya sace su, in ji kakakin ‘yan sndan.

SP Kiyawa ya ƙara da cewa, bayan matashin ya gano cewa matar ta gane shi, sai ya yi amfani da tavarya ya yi ta buga mata a kai, haka kuma ya buga wa ‘ya’yanta biyu taɓaryar sa’annan ya gudu da wayoyin.

Bayan gudanar da wannan aika-aika ne mijin matar ya je ya samu matarsa ta rasu da kuma ‘ya’yansa sun samu rauni wanda hakan ya sa ya garzaya domin bayar da rahoto ga ‘yan sanda.

Ko da ‘yan sanda suka samu rahoton, sai suka haɗa kai da hukumar tsaro ta farin kaya wato DSS har ta kai ga sun kama Abdulsamad Suleiman.

Bayan gudanar da bincike Abdulsamad ya shaida wa ‘yan sandan cewa ya sayar da wayoyi biyu kan Naira dubu 12 sa’annan ɗayar wayar kuma ya bai wa wani abokinsa mai suna Mu’azzam Lawan ɗan shekara 17.

‘Yan sandan sun ce tuni aka kama Mu’azzam ɗin inda shi ma ya ce ya sayar da wayar kan Naira dubu biyu.

Rundunar ‘yan sandan ta ce da zarar an kammala bincike za a gurfanar da waɗanda ake zargin a gaban kotu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *