Daga MAHDI M. MUHAMMAD
A ranar Juma’a Hukumar Ƙwallon Ƙafar Turai (UEFA) suka fitar da jadawalin matakin ƙungiyoyi takwas ɗin ƙarshe na Gasar Zakarun Turai.
A ƙunshin jadawalin, Real Madrid za ta fafata da Chelsea a matakin daf da na kusa da na ƙarshe a babbar gasar Turan ta bana.
Ko a kakar da ta gabata, ƙungiyoyin sun haɗu a irin wannan matakin inda Real Madrid ta samu nasara a kan Chelsea.
A bana dai Real ta kawo wannan matakin, bayan da ta fitar da Liverpool da cin 6-2 gida da waje a kakar bana.
Ita kuwa Chelsea ta yi nasarar yin waje da Borussia Dortmund da cin 2-1 gida da waje.
Mai riƙe da Firimiyar Ingila, Manchester City za ta kara da Bayern Munich, mai gasar Zakarun Turai shida.
Inter Milan za ta yi tata burza da Benfica, mai riƙe da kofin Serie A, inda ita kuma AC Milan za ta fuskanci Napoli.
Idan Chelsea da Manchester City su kai zagayen gaba, ke nan za su iya haɗuwa a daf da ƙarshe, wataƙila AC Milan ko Napoli ta fuskanci Inter Milan ko Benfica a ɗaya wasan daf da ƙarshe.
Jadawalin wasannin:
- Inter Milan da Benfica
- Real Madrid da Chelsea
- Manchester City da Bayern Munich
- AC Milan da Napoli
Wasannin daf da na kusa da na ƙarshe:
Ranar 11 ga watan Afirilun 2023;
- Inter Milan da Benfica
- Real Madrid da Chelsea
Ranar 12 ga watan Afirilun 2023;
- Manchester City da Bayern Munich
- AC Milan da Napoli
Real Madrid ce za ta fara karbar baƙuncin Chelsea a Santiago Bernabeu a wasan farko ranar 11 ga watan Afirilu.
Sannan Chelsea ta karɓi baƙuncin wasa na biyu a Stamford Bridge ranar 19 ga watan Afirilu.
Chelsea tana da Champions League biyu, ita kuwa Real ita ce mai riƙe da na bara kuma na 14 jimilla.
Za a fara buga wasannin farko ranar Talata 11 da kuma Laraba 12 ga watan Afirilu, sannan a yi wasa na biyu tsakanin 18 da kuma 19 ga watan Afirilu.
Za a fara wasan farko a daf da ƙarshe daga ranar 9 da 10 ga watan Mayu, sannan a buga zagaye na biyu ranar 16 da 17 ga watan Mayu.
Za a buga wasan ƙarshe ranar Asabar 10 ga watan Yunin 2023 a Istanbul a filin wasa Ataturk Olympic Stadium.