Yadda taron ƙaddamar da littafin ‘Wazirin Ilorin’ ya gudana

Daga AISHA ASAS

A ranar Lahadin da ta gabata 14 ga Nuwamba, 2021 ne aka ƙaddamar da littafin Wazirin Ilorin, Sanata Dr. Olusola Abubakar Saraki, wato mahaifi ga tsohon shugaban majalisar dattawan Nijeriya, wanda ƙungiyar Manyan Marubuta Tarihi da Harsunan Afrika, ƙarƙashin jagorancin shugaban kungiyar Farfesa Khalid Abdullahi Zariya, ta shirya wa kafafen yaɗa labarai a Agura Otel, don jin ta bakin mawallafin littafin.

Taron ƙaddamar da littafin wanda aka rubuta akan rayuwa, gwagwarmaya da faɗi-tashin da Marigayi Sanata Dr. Olusola Abubakar Saraki (Wazirin Ilorin) ya yi a fannin siyasa da gina al’umma tare da sauran ɓangarori da marubucin ya taɓo a cikin rayuwar sa.

Wannan taro dai ya zo da wani sabon salon ƙaddamar da littafi a duniyar rubutu da marubuta, inda maimakon a ga manyan ‘yan kasuwa, ‘yan siyasa da masu hannu da shuni suna ɗiban kwafin da suke buƙata suna saye akan maƙudan kuɗaɗe; sai aka tara ‘yan jaridu da abokan arziki don gabatar da ƙasurgumin littafin ga al’umma.

Da farko dai taron ya samu tubarrakin buɗewa da addu’a daga bakin wakilin limamin masallacin Al-Ansarul Ismam, inda ya yi addu’a da fatan taro ya gudana lafiya a kuma kammala shi lafiya. 

Daga bisani kuma aka nemi mai gayya mai aiki, wato mawallafin littafin, Farfesa Khalid Abdullahi don gabatar da littafin da kuma jawabinsa ga ‘yan jaridun da suka halarci taron.

Farfesa Khalid ya fara da yaba wa, da kuma jinjina wa ‘yan jarida akan namijin ƙoƙarin da su ke yi wurin isar da sahihan labarai ga al’umma. Ya kuma yi tsokaci kan qalubalen da ‘yan jarida ke fuskanta a rayuwar aikin nasu.

Mawallafin littafin ya bayyana dalilin sa na zaɓen tattaunawa da ‘yan jarida a wannan rana maimakon tara mutane don yin kasuwancin littafin a zamanance wato ‘launching’, inda ya ke cewa, ” ‘yan jarida na da amana, domin aikin su ne hakan, duk wani abu da ka ba wa ɗan jarida zai isar da shi ga al’umma, shi ya sa na zaɓe gayyatar su a wannan rana.”

Farfesa Khalid Abdullahi

Farfesa Khalid Abdullahi ya ci gaba da jarabinsa kan maƙasudin taron wato littafin da ya wallafa, ya fara da yin tsokaci da kuma tsakuro kaɗan daga cikin tarihi da gwagwarmayar Marigayi Sanata Olusola Saraki (Wazirin Ilorin), inda ya bayyana cewa, “An haifi Marigayi Sanata Dr. Olusola Abubakar Saraki ranar Laraba 17 ga Mayu, 1933 a Ilorin ta Jihar Kwara da ke tsakiyar Arewacin Nijeriya, wanda shi ne ya fi shahara da yin fice bisa muƙamin sarautar Wazirin Ilorin a zamanin rayuwarsa ta shekara 79.”

Farfesa ya ci gaba da cewa, “Sanata Dr. Olusola Saraki mutumin kirki ne nagartacce, kuma mai kallon kowa da daraja cikin mutunci, kuma bai taɓa raina kowa ko yi wa wani ko wata kallon banza ba, kuma ba a san shi da yin tozarci ko izgili ko wulaƙanci ga kowa ba, komai talauci ko ƙarancin ilimin mutum.” 

Sai dai ko kafin nan, Farfesa Khalid Abdullahi Zariya ya bayyana cikakken maƙasudin da suka ja ra’ayinsa ga soma yin wannan aiki na taskace tarihin Wazirin Ilorin, inda ya nuna kishin sa ga al’ummar Arewa masu fahimtar harshen Hausa musamman matasa masu kwaɗayin son gudanar da mulki da jagorancin al’umma cikin adalci da tausayi da nufin duban rayuwar Marigayi Dr. Olusola Abubakar Saraki a matsayin madubin dubawarsu.

Tun da farko dai Farfesa Khalid Abdullahi Zariya a cikin littafin Tarihin Wazirin Ilorin da ya wallafa, ya bayyana cewa, “na yi tunanin gudanar da aikin taskance tarihin Wazirin Ilorin, Sanata Dr. Olusola Abubakar Saraki, waje guda ne, kuma cikin harshen mutanen Arewa; wato harshen Hausa, da nufin samar da littafin da na ke fatan zai zama babban alheri abin ƙaunar son karantawa musamman ga matasa da ke fatan wanyewa lafiya a matsayin shugabanni nagari, masu kyakkyawar niyyar bada gudummuwa ta hanyar sadaukar da lokaci da rayuwarsu da nufin samar da cigaban alheri da bunƙasa gami da haɓaka ga tattalin arzikin Nijeriya da na al’ummarta ba tare da nuna wariya ko son kai ko ganin ƙyashi ko mugunta da handama ba.”

Da ya ke amsa tambayoyin manema labarai, Farfesa Khalid ya tabbatar da cewa, ba ya rubutu kan wanda bai cancanta ba, inda ya ke cewa, “ba na rubuta tarihin mutane don in tallata su, ina rubuta tarihin mutanen da suka damu da rayuwar al’ummar su a lokacin da su ke raye, ko suka damu da addinin al’ummar su, ko suka yi wa addinin al’ummar su hidima, ko suka yi wani aiki da al’ummar su ke cin gajiyar aikin ko da mutanen ba su san su suka yi ba.”

Da ya ke amsa wata tambayar kan dalilin da ya sa shi sha’awar rubutu kan tsohon shugaban ƙungiyar dattawan Arewa, Farfesa Khalid Imam ya amsa da cewa, “babban abin da ya sa ni sha’awar rubutu kan Sanata Dr. Olusola Abubakar Saraki, shi ne irin yadda ya kasance kamar a kan iyakar Arewa da Kudu, sannan rayuwarsa ma gabaɗaya a Kudu, amma tunaninsa ya fi a Arewa, sannan tausayinsa ga Arewa, waɗanda ma suke ƙarshen Arewa. Ya yi ayyuka ga ‘yan Arewa ma su yawa wanda ya kamata su sani, kuma su gode masa. Wannan ne dalili da ya sa na rubuta wannan littafin.”

Taron ya samu halartar kafafen yaɗa labarai da dama da suka haɗa da: Muryar Amurka VOA, Rediyo Faransa RFI, Leadership, Blueprint Manhaja, NTA, Liberty, Voice of Nigeria da sauransu.

Daga ƙarshe Shugaban ƙungiyar, kuma mawallafin littafin Farfesa Khalid Zariya, ya raba wa mahallarta taron littafin kyauta, a ƙoƙarinsa na gode ma su da kuma yaba wa da lokacinsu da suka bayar.