Yadda ’yan kasuwa suka mayar da titinan Zariya wurin kasuwanci

Daga MOH’D BELLO a Zariya

Yanzu haka ƙananan ‘yan kasuwa sun maida sababbin titituna da gwamnati jihar Kaduna ta kammala wajen kasuwanci a birnin Zariya dake ƙaramar Hukumar ta Zariya.

Wakilinmu wanda ya leƙa kasuwar ya ruwaito cewa ƙananan ‘yan kasuwar waɗanda da suka haɗu da masu sayar da kayan miya da ma’auna da mahauta har da masu sayar da man fetur a cikin galoli duk su ne suka mamaye sabo titin da ya tashi daga Ƙofar gidan Bellon Gima ya ratsa Kusfa zuwa Azaran Dabuwa da titin da ya tashi daga Ƙofar Gidan Bellon Gima zuwa Unguwar Ƙaura ta zarce kasuwar Amaru domin cin kasuwancinsu.

Wasu waɗanda suka zanta da wakilin Manhaja sun ce, “son zuciya ne kawai na ‘yan kasuwar saboda ga shaguna amma sun ƙi kamawa sun gwammace su kasa kayansu a titunan saboda taran kwastomomi tare da haɗama.

“Da kuma rashin sanin haƙƙoƙin jama’a duba da yadda ababen hawa ke kaiwa da komowa akan titin.”

Wani mazaunin kusa da kasuwar cikin birnin Zariya mai sana’ar shinkafa, Mallam Sani Garba ya ce rashin bin doka da oda ne tare da sakacin hukumomi ya janyo haka.

Ya ce  “wannan kasuwanci a titi babbar illa ce, domin tana iyar haifar da matsala la’akari da yawan ababen hawa da ke kaiwa da komawa, a ce ana kasuwanci a titi ga kuma masu sayar da man fetur a galoli, Allah ne kawai Ya san irin asarar rayuka da dukiya ranar da aka samu wani hadari a wajen.”

Wakilinmu ya leƙa kasuwar Tudun Wada dake Ƙaramar Hukumar ta Zariya nan ma ‘yan kasuwar sun mamaye titin Ahmed Mohamed Maƙarfi wanda shine babban titin da ya ratsa Zariya da Kaya saboda aikin sabunta kasuwar da ake yi a halin yanzu.

Idan za a iya tunawa ƙarshen shekarar bara Hukumar Kula da Muhalli (KEPA) da Hukumar Tsara Birane (KASUPDA) ta Jihar suka tashi ‘yan kasuwar daga titunan, amma cikin wannan shekarar suka dawo kan titunan.