‘Yan sanda na bincike kan budurwar da ta rataye kanta a Kano

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano tana ci gaba da bincike kan abin da ya sa wata budurwa mai shekara 17 ta rataye kanta a ƙauyen Garin Dau da ke yankin ƙaramar hukumar Warawa.

Mafi akasarin mazauna ƙauyen dai sun yi zargin cewar budurwar ta rataye kan nata ne bisa auren dole da iyayenta ke shirin yi mata.

Sai dai iyayen nata sun musanta wannan zargi inda suka ce ba ta kammala makarantar sakandare ba, balle a yi maganar aurar da ita.

Faruwar wannan lamari dai ya zo wa mazauna yankin da mamaki, sakamakon yadda da dama daga cikin mutanen ƙauyen ke bayyana budurwar da kyawawan ɗabi’u.

A yau ne aka shiga yini na biyar na rasuwar Safiya mai shekaru 17 da ke aji biyu a makarantar sakandare, wadda aka tarar da gawarta a rataye kuma ana zargin ita ta rataye kanta.

SP Abdullahi Haruna Kiyawa shi ne mai magana da yawun rudunar ‘yan sanda a Kano, ya shaida wa BBC cewa sun samu labarin faruwar lamarin, kuma suna bincike kan lamarin don gano shin budurwar ce ta rataye kan nata ko kuwa.

Wannan dai shi ne rahoton rataye kai na baya-bayan nan da aka samu a Kano, savanin a watannin baya da suka gabata, biyo bayan kiraye-kiraye da wayar da kan al’umma da hukumomin jihar suka ɗauka.

A mafi akasarin lokuta ƙwararru a fannin sanin halayyar ɗan adam na alaƙanta ɗabi’ar mutum ya rataye kansa, sakamakon ciwon damuwa da yake fama da shi, ko wata larura da ta shafi ƙwaƙwalwa.