‘Yan siyasar Amurka ba su maida hankali kan haƙƙin bil Adam a ƙasar ba

Daga CMG HAUSA

A jiya ne, aka yi harbe-harbe a wani shagon zamani na Walmart dake birnin Chesapeake na jihar Virginia na Amurka, lamarin da ya haddasa mutuwa da jikkatar mutane da dama.

Wannan ya sa yawan harbe-harben da aka yi a Amurka ya haura 600 a cikin shekaru 3 a jere.

Yawan al’ummar Amurkawa ya kai kashi 4.2% na al’ummar duniya, yawan bindigar da suke mallaka ya kai kashi 46% na masu rike da bindiga a duniya.

Hakan ya sa, Amurka ta zama kasa mafi samun masu fama da haɗarin bindiga a duniya. Bayanai na baya-bayan da shafin Intanet mai nasaba da bayanai masu fama da harbe-barhen bindiga na Amurka, sun nuna cewa, ya zuwa ran 21 ga wannan watan, yawan mamata sakamakon harbe-harbe a ƙasar ya kai fiye da dubu 39, ‘yancin rayuwa, shi ne mafi muhimmanci ga ɗaukacin bil-Adama, ko gwamnati za ta iya hana aukuwar wannan hadari, shi ne wani ma’aunin tabbatar da hakkin Bil Adam.

Mai fassara: Amina Xu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *