Zaɓen 2019: Lauyoyi sun nemi APC ta biya su haƙƙinsu a Kano

Daga FATUHU MUSTAPHA

Wata tawagar lauyoyi a jihar Kano ta yinƙura neman haƙƙinta daga hannun jam’iyyar APC reshen jihar na aikin da ta yi mata yayin zaɓen 2019.

A wata wasiƙa da suka aika wa APC ta hannun lauyansu Usman Umar Fari, lauyoyin da lamarin ya shafa sun buƙaci jam’iyyar ta hanzarta biyansu kuɗeɗen aikin da suka yi mata yayin babban zaɓe na 2019.

Lauyoyin sun ce kuɗin da suke nema a biya su, haƙƙin aikin da suka yi wa APC ne kan batutuwan da suka shafi sha’anin shari’ar zaɓe.

Lauyan lauyoyin, Usman Fari, ya ja hankalin jam’iyyar kan cewa ƙin biyan lauyoyin kuɗeɗensu, hakan zai sa su ɗauki matakin shari’a don ƙwato haƙƙinsu.

Wasiƙar lauyoyin zuwa ga APC ta nuna yadda lauyoyin suka yi aikin kare APC a shari’u daban-daban kuma suka yi nasara alhali ba a biya su haƙƙin aiki ba.

Binciken Manhaja ya gano cewa, kafin wannan lokaci lauyoyin sun rubuta takarda da dama a lokuta daban-daban zuwa ga APC suna neman a biya su haƙƙinsu amma hakan bai samu ba.

Sai dai wata majiya mai tushe ta faɗa cewa, lauyoyin da suka yi aikin kare Gwamna Abdullahi Umar Ganduje a zaɓen na 2019 a kotun sauraron ƙararrakin zaɓe, tuni an biya su kuɗaɗensu, musamman ma lauyoyin da aka yi hayarsu daga wajen jihar.