Za a yi zaben gwamnan Anambara ran 6 ga Nuwamba – INEC

Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta bayyana cewa a ranar 6 ga Nuwamba, 2021 za a yi zaben gwamnan Jihar Anambara.

Hukumar ta bayyana jadawalin ranar zaben da abubuwan da za a aiwatar ne a cikin wata sanarwa da ta bayar a ranar Talata a Abuja.

Shugaban Kwamitin Yada Labarai da Wayar da Kan Masu Zabe na hukumar, Mista Festus Okoye, wanda ya bada sanarwar, ya ce hukumar ta yi wani zama a ranar Talata inda ta tattauna kan zaben na Anambara.

A cewar sa, za a yi zabubbukan share fage tare da warware duk wani sabani da ka iya tasowa a tsanakin ranar 10 ga Yuni zuwa ranar 1 ga Yuli.

Ya ce, “Kamar yadda Sashe na 178(1) da (2) na Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya na 1999 (kamar yadda aka gyara shi) da Sashe na 25(7) da (8) na Dokar Zabe ta 2010 (kamar yadda aka gyara ta) su ka tanadar, ba za a gaza gudanar da zaben mukamin Gwamnan Jiha a cikin kwana 150 kasa da ko kuma kwana 30 sama da karewar wa’adin mulkin wanda ya rike mukamin ba.

“A Kundin Tsarin Mulki da kuma Doka, wa’adin mulkin gwamnan Anambara zai kare ne a ranar 17 ga Maris, 2022, saboda haka rana mafi kusa da za a iya yin zaben na Gwamnan Anambara za ta kama 18 ga Oktoba, 2021 sannan ba za a zarce ranar 15 ga Fabrairu, 2022 ba don a yi zaben.

“A bisa ikon da Tsarin Mulki da Dokar Zabe da sauran dokoki su ka ba ta a wannan lamari, INEC ta saka ranar 6 ga Nuwamba a matsayin ranar da za a yi zaben Gwamnan Anambara.”

Mista Okoye ya kara da cewa, “Don haka, yanzu Hukumar ta fitar da jadawalin lokutan zabe da sauran ayyuka na zaben.

“Bisa ga wannan jadawalin lokutan zabe da ayyukan da su ka jibince shi, hukumar za ta fitar da sanarwar dokar gudanar da zaben a ranar 9 ga Yuni.

“Za a gudanar da karbar fom mai lamba EC9 (wanda a da ake kira CF001) da fom mai lamba EC9B (wanda a da ake kira CF002) don shiga zaben a ranar 10 ga Yuni, sannan za a gudanar da zabubbukan share fage da warware sabanin da ka iya tasowa a tsakanin ranakun 10 ga Yuni da 1 ga Yuli.”