Ƙarfafa yaƙi da cin hanci da rashawa

Mataimakin Shugaban Ƙasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana cewa, cin hanci da rashawa a matsayin barazana ga cigaban Nijeriya tare da yin kira da a ɗauki matakin gama gari a kan matsalar. Ya kuma hori ’yan Nijeriya da su guji cin hanci da rashawa, su rungumi gaskiya, su haɗa kai domin gina ƙasa mai inganci bisa gaskiya da riƙon amana.

Mataimakin shugaban ƙasar, wanda ya bayyana hakan a Abuja a taron ƙaddamar da hukumar yaƙi da yi wa tattalin arzikin qasa zagon ƙasa (EFCC) a hukumance na ƙungiyar makarantu, ya jaddada cewa duk wani cin hanci da rashawa a matsayin laifin da zai kawo matsala ga cigaban al’umma da kuma waɗanda ma ba a haifa ba. Ya ce, duk wani jami’in gwamnati da ya yi sata, yana wa sace wa al’ummar Nijeriya kuɗaɗen da suka shafi kiwon lafiya, ilimi, inda ya ƙara da cewa dole ne ’yan ƙasa su zama jami’an da ke yaƙi da cin hanci da rashawa, walau a gwamnati ko kuma a matsayin masu zaman kansu.

Ko shakka babu, Osinbajo ya yi magana mai ma’ana kan illar cin hanci da rashawa da kuma buƙatar da ke akwai na dukkan ’yan Nijeriya su rungumi yaƙi da wannan dodo. Don haka ne ma ya zama wajibi a ƙarfafa hukumomin yaqi da cin hanci da rashawa da kuma dokokin yaƙi da cin hanci da rashawa a duk wani mataki na sa. Idan babu cibiyoyi masu ƙarfi da tsauraran dokoki na yaƙi da cin hanci da rashawa, yaƙi da cin hanci da rashawa zai zama yaudara ne kawai. Wannan shi ne karo na biyu da mataimakin shugaban ƙasar ke jan hankali kan illar cin hanci da rashawa a cigaban al’umma. A farkon watan Janairu, ya yi kira da a fallasa tare da yin Allah wadai da cin hanci da rashawa a matsayin sharuɗɗa na biyan buƙatun jama’a ga ƙasar.

Mun yarda da Osinbajo cewa a lokacin da jami’an gwamnati, babba ko ƙarami a ɓangaren zartarwa, majalisa ko na shari’a suka zama ƙofofin cin hanci da kwasar kuɗin jama’a, to lallai sai an sha wahala a mulkin ƙasa. Bayan ƙaddamar da wannan shiri na abin yabawa, dole ne gwamnati ta tashi tsaye wajen kamawa tare da gurfanar da masu hannu a cikin almundahana tare da tabbatar da hukunta masu aikata laifuka. Ta yin hakan ne zai nuna cewa har yanzu yaqin da ake yi da sata yana nan ƙam. Za mu iya aron ganye daga ƙasashen Asiya, irin su Chana da Japan, kan yadda za a yi yaƙi da cin hanci da rashawa.

Duk da iƙirari da jami’an gwamnati ke yi na daƙile wannan matsala, a bayyane yake cewa cin hanci da rashawa na cigaba da ƙaruwa a ƙasar. Bayan cin hanci, rashawa yana bayyana ta wasu hanyoyi kamar hauhawar farashin kwangila, kasafin kuɗi, maguɗin zaɓe da kuma lalata tsarin mulki da gangan. Mun amince da cewa gwamnati ta yi ƙoƙarin magance matsalar ta hanyar kafa tattalin arziki da kuɗi. Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa (EFCC), da hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa mai zaman kanta (ICPC) da sauran su, sun samu wasu nasarori a yaƙin. A cewar shugaban hukumar ta EFCC, Abdulrasheed Bawa, hukumar ta samu wasu laifuka guda 3,440 akan laifukan kuɗi da yanar gizo a faɗin ƙasar nan daga watan Janairu zuwa Nuwamba 2022. A shekarar da ta gabata, ta samu jimillar laifuka 2,220 a faɗin ƙasar. Hukumar da ke yaƙi da cin hanci da rashawa ta ce, ta kwato kusan dala miliyan 750 na kuɗaɗen cikin gida da na waje daga hannun ’yan damfara. Duk da haka, akwai sauran damar ingantawa.

Duk da nasarorin da aka samu, alƙaluman hasashen cin hanci da rashawa a Nijeriya ya qara taɓarɓarewa. Ya zuwa shekarar 2021, wata ƙungiyar farar hula mai suna YIAGA Africa, ta nuna cewa Nijeriya ta yi asarar aƙalla dala biliyan 582 tun bayan samun ’yancin kai saboda cin hanci da rashawa. Daga cikin kuɗaɗen, an ce an karkatar da kimanin Naira tiriliyan 1.3 na dukiyar al’umma a tsakanin shekarar 2011 zuwa 2015 kaɗai. Kimanin Naira Tiriliyan 5.2 ne aka yi hasara ta hanyar almundahana a tashoshin jiragen ruwa a cikin wannan lokaci. Har ila yau, a cikin qididdigar da aka yi wa laƙabi da ‘Transparency International 2021 CPI’, Nijeriya ta kasance a matsayi na 154 a cikin ƙasashe 180 da aka gudanar da bincike a kan lamarin, wanda ya sa ta zama ƙasa ta biyu mafi cin hanci da rashawa a yammacin Afirka. Matsayin ya nuna cewa Nijeriya ta ragu daga 149 a cikin 2020, shekara ta biyu a jere na raguwa akan darajar CPI.

Yayin da Mataimakin Shugaban ƙasar ya yi kira da a ɗauki matakin haɗin gwiwa a kan cin hanci da rashawa, ya zama wajibi gwamnati, wadda ita ce a kan mulki, ta ceto ƙasar nan daga halin da ake ciki. Wani abin sha’awa shi ne, gwamnatin ta lissafa yaƙi da cin hanci da rashawa a cikin manyan manufofinta.

Duk da cewa babu wata ƙasa da ta kuvuta daga cin hanci da rashawa, amma tamu ta zama annoba. Ƙasar ba za ta iya cigaba a cikin cin hanci da rashawa ba. Yakamata gwamnati ta yaƙi matsalar gaba ɗaya. Shugabanninmu su nuna misali mai kyau game da wannan, kuma su yi Allah wadai da ayyukan rashawa. Bai kamata a riƙa zaɓar jami’an da ke cin hanci da rashawa ba. A yi kira ga ‘yan Nijeriya da su haɗa kai su yaƙi cin hanci da rashawa. A tsara manufofi don duba shi. Akwai buqatar a ƙaƙaba takunkumin da ya dace kan cin hanci da rashawa. Cin hanci da rashawa na ƙaruwa a ƙasar ne saboda rashin isassun matakan daƙile shi. Abin da ya sa muke buƙatar ƙarin tsauraran dokoki game da barazanar kenan.