Ƙasar Sin ta yi kira da a kyautata tafiyar da harkokin tattalin arziki a duniya

Daga CRI HAUSA

Ma’aikatar kuɗi ta ƙasar Sin, ta yi kira ga ƙasashen duniya su ƙarfafa haɗin gwiwa wajen tafiyar da dabarun da suka shafi tattalin arziki, a matsayin wata hanya ta samun ci gaba na bai ɗaya.

Ministan kuɗi na ƙasar Sin, Liu Kun ne ya bayyana haka, yayin wani taron ministocin kuɗi da gwamnonin manyan bankunan ƙasashen G20 da ya gudana ta kafar bidiyo.

A cewar Liu Kun, cikin ƙasashen ƙungiyar G20, ƙasar Sin ta kasance babbar mai bayar da gudunmuwa ga shirin sauƙaƙa basussuka ga ƙasashe masu fama da talauci.

Ya ce ƙasar Sin tana kira ga dukkan masu ruwa da tsaki, su aiwatar da matsaya da G20 ta cimma, su girmama cikakken ‘yancin ƙasashen da ake bi bashi, su kuma inganta nasarar wannan batu a aikace.

Ya ce ya kamata masu bayar da bashi ga ɓangarori daban-daban kamar Bankin Duniya, su ɗauki matakan sauƙaƙa basussuka bisa hanyoyi masu ƙarfi, da taimakawa ƙasashe masu ƙarancin kuɗin shiga.

Fassarawa: Fa’iza Mustapha

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *