Ɗan Sarauniya ya shawarci Ganduje ya koma makarantar allo

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Tsohon kwamishinan ayyuka na jihar Kano Injiniya Mu’azu Magaji, ya shawarci gwamnan Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya koma makarantar allo domin koyon yadda ake tafiyar da al’umma, tare da sanin matsayin iyali a tsari na tafiyar da mulki.

Wannan na zuwa ne daidai lokacin da gwmnatin Kano ta fitar da sanarwa Gwamna Ganduje ya tafi ƙasar Amurka domin ɗaukar kwas kan yadda ake gudanar da mulki a jami’ar Harvard.

Cikin wani rubutu da Muazu Magaji wanda aka fi sani da Ɗan Sarauniya ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya ce a wannan lokaci Gwamna Ganduje ba ya buƙatar ƙarin wani ilimi daga Jami’ar Havard dake ƙasar Amurka, domin kuwa karatuttukan  da yake da su daga Jami’ar Ahmadu Bello Zariya da Jami’ar Ibadan sun ishe shi, illa yana buƙatar ilimin da ya rasa tun a baya wato ilimin makarantar allo.

A cewar Ɗan Saurauniya ta haka ne Ganduje zai gane yadda ake tafiyar da dukiyar al’ummar da ake shugabanta da kuma amfanin naɗa mataimaka wanda za su taimaka masa wajen gudanar da mulki nagari.

Sannan ya buƙaci Gwamna Ganduje ya nemi tarihin Sayyadina Umar domin jin salon shugabancin sa, wanda idan ya yi haka to baya buƙatar zuwa Jami’ar Harvard domin samun ilimin shugabanci.

Idan dai za a iya tunawa a watan Afrilun shekarar 2020 ne dai Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya kori Injiniya Mu’azu Magaji daga muƙamin kwamishan ayyuka biyo bayan wasu kalamai da ya yi wanda ke nuna cewa na murna da rasuwar tsohon shugaban ma’aikata na Fadar Shugaban Ƙasa, Malam Abba Kyari.

Gwamna Ganduje ya sake naɗa Ɗan Sarauniya a matsayin shugaban kwamitin aikin janyo bututun gas daga Ajaokuta zuwa Kaduna zuwa Kano, inda a nan ma Ganduje ya kore shi sakamakon rashin taɓuka wani abu, a cewar Gandujen.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *