27
Feb
Daga BASHIR ISAH Hukumar Alhazai ta Nijeriya (NAHCON) ta kore batun da aka yi ta yayatawa wai ta samu kujerun Hajji daga Gwamnatin Saudiyya na Hajjin bana. Sanarwar da hukumar NAHCON ta fitar a Juma'ar da ta gabata wadda ta samu sa hannun shugabar sashen hulɗa da jama'a ta hukumar, Fatima Sanda, ta nuna hankalin hukumar ya kai ga wani saƙon talla da aka yi ta yaɗawa a soshiyal midiya kan cewa Nijeriya ta samu gurbin mahajjata 50,000 na Hajjin 2021/1442 AH a hukumance. Tallar ta buƙaci maniyyata Hajji suna iya soma ajiyar wani kaso na kuɗi don sayen kujerar…