2023: Ba za mu bari rikicin cikin gida ya hana APC cin zaɓen Shugaban Ƙasa ba – Gwamna Sani Bello

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Gwamnan Jihar Neja, kuma shugaban ƙungiyar gwamnonin arewa ta tsakiya (NCSGF), Abubakar Sani Bello ya bayyana cewa, har yanzu dai yana  kan bakarsa wajen ganin jam’iyya mai mulki, APC ta kai bandenta a kakar zaɓe mai zuwa tun daga kan matakin shugabancin ƙasa, zuwa jihohi har zuwa kan ƙananan hukumomi.

Waɗannan bayanai sun fito ne daga bakin Sakataren watsa labarai na gwamnan Jihar Neja, Mary Noel-Berje. An gabatar da bayanan ne a yayin amsar baƙuncin wasu wakilai daga Sanata Dakta George Akume zuwa ga gidan gwamnatin na jihar Neja.

A nasa jawabin, shi ma Gwamna Sani Bello ya bayyana cewa, ya kamata a yi adalci ga arewa ta tsakiya wajen rarraba muƙaman siyasar ƙasar nan. 

Gwamnan ya ƙara da cewa, an mayar da yankin Arewa ta tsakiya tamkar saniyar ware wajen rarraba ayyukan more rayuwa a ƙasar nan. Musamman ma kasancewarsu a tsakanin yankunan Kudu da Arewacin ƙasar nan. A cewar sa ma, sam ba a ko duban su duk da yadda suke bada gudunmuwar ƙuri’u a lokacin zaɓuɓɓuka.

A cewar sa, da a ce gwamnati za ta dubi yankin nasu na Arewa ta tsakiya, ta ba wa sashen nomansu kulawar da ta kamata, to da ba makawa zai iya ciyar da ƙasar nan da ma Afirka ta yamma gabaɗaya hankali a kwance. 

Daga ƙarshe ya ba da tabbacin bada dukkan gudunmuwa da goyon baya ga dukkan wani ɗan takara da ya fito daga yankin nasu ba ma kawai don samun haɗin kan jam’iyya ba, har ma domin APC ta kai ga samun nasara a zaven 2023.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *