Gwamnatin Zamfara ta ba da tallafin miliyan N15 ga iyalan ’yan sanda 13 da aka kashe

Daga SANUSI MUHAMMAD, a Gusau

Gwamnatin jihar Zamfara ta bayar da gudummawar zunzurutun kuɗi har Naira miliyan 15 ga iyalan jami’an ‘yan sandan Nijeriya da aka kashe a wani kwanton ɓauna da wasu ‘yan bindiga suka yi a makon da ya gabata a ƙauyen Kurar Mota da ke ƙaramar hukumar Bunguɗu ta jihar.

Kwamishinan Yaɗa Labarai na Jihar, Ibrahim Magaji Dosara ne ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa da aka miƙa wa Manhaja a Gusau, ranar Juma’a.

A cewar sanarwar, kowanne daga cikin iyalan wadanda suka mutu za su karɓi Naira miliyan ɗaya, yayin da za a bai wa iyalan waɗanda suka samu raunuka a lokacin harin Naira miliyan 2. Tuni dai, gwamnati ta kula da kuɗaɗen magungunansu a asibiti.

A cewar gwamna Bello Muhammed Matawalle, karamcin na daga cikin alƙawuran da gwamnatinsa ta yi tun da farko don taimaka wa iyalan jami’an tsaron da suka rasa rayukansu a bakin aiki s jihar.

“Tun lokacin da ya hau ƙaragar mulki, Gwamna Matawalle ya kasance yana da kyakkyawar alaƙa da jami’an tsaro kuma gwamnatinsa tana taimaka wa hukumomin wajen sauke nauyin da ke kansu”, in ji sanarwar.

Idan za a iya tunawa Gwamna Bello Matawalle ya ziyarci jami’an ‘yan sanda da suka samu raunuka a asibiti don jajanta musu kan wannan mummunan lamari.