Sin: Amurka da ƙasashen Yamma suka haddasa matsalar ‘yan gudun hijira ke cigaba da taɓarɓarewa

Daga CMG HAUSA

Ranar 20 ga watan Yuni, rana ce ta ‘yan gudun hijira ta duniya karo na 22. Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen ƙasar Sin Wang Wenbin, ya bayyana a wannan rana cewa, wasu ƙasashen yammacin duniya bisa jagorancin Amurka, sun daɗe suna haddasa yake-yake da hargitsi, da tsoma baki a harkokin cikin gidan wasu ƙasashe, da haifar da matsaloli na jin kai. Su ne suka fara haddasa matsalar ‘yan gudun hijira.

Rahotanni sun bayyana cewa, a ranar 17 ga wata, ƙasar Birtaniya ta amince da miƙa mutumin da ya kafa shafin kwarmata bayanai mai suna, wato WikiLeaks Assange zuwa kasar Amurka. Kan wannan batu Wang Wenbin ya ce, shari’ar Assange tamkar wani madubi ne, kuma hakan na nuni da yadda ƙasashen Amurka da Birtaniyya suke munafurcin da’awar tabbatar da ‘yancin ‘yan jarida.

Wang Wenbin ya ƙara da cewa, yayin da ake ci gaba da bullo da tsare-tsare masu yawa da ke daidaita tsarin rigakafin cututtuka da shawo kan annoba yadda ya kamata, da ci gaban tattalin arziki da zamantakewar al’umma, yadda tattalin arzikin ƙasar Sin ke ci gaba da gudana, ya sa ƙasashen duniya kara amincewa da ci gaban tattalin arzikin ƙasar Sin.

Mai fassarawa: Ibrahim daga CMG Hausa