A karo na biyu, NLC ta sake ƙin amincewa da yin rajista ga ƙungiyoyin CONUA da NAMDA

Daga AMINA YUSUF ALI

Ƙungiyar Ƙwadago ta Nijeriya (NLC) ta sake yin watsi da ƙudirin Ministan Ƙwadago na Nijeriya a kan yin rajistar sabbin ƙungiyoyin malaman makaranta a jami’o’in Nijeriya.

Wannan bayani yana ƙunshe ne a wata takarda wacce shugaban ƙungiyar NLC Ayuba Wabba ya gabatar ga Ministan Ƙwadago da ayyuka, Chris Ngige.

Wannan takarda tana a matsayin wasiƙar da ministan ya aiko yana neman ƙungiyar NLC ɗin ta ba da shaidar rajista ga ƙungiyoyin Ƙungiyar Jami’o’in Nijeriya (CONUA) da kuma Ƙungiyar Malaman koyar da likitan da likitancin haƙori na Nijeriya (NAMDA).,

Wabba ya bayyana cewa, akwai ayar tambaya a game da rajistar da ake son a yi wa ƙungiyoyin CONUA da NAMDA, shin haɗe kan ƙungiyoyi Ministan yake nufin yi ko kuma dai ƙungiyoyin da suka nemi hukumar ta NLC ta yi wa rajista tun a shekarar 2018 a matsayin ƙungiyoyin kasuwanci suke son cigaba da yi wa rajistar?

A cewar sa, wannan buƙata ta Ministan ta saɓa wa dokar Nijeriya ta sashe na 3(2) na dokar ƙunyoyin kasuwanci a kundin tsarin mulkin Nijeriya. Dokar ta ce: “Ya haramta a yi wa wata sabuwar ƙungiya rajista don ta wakilci wasu ma’aikata bayan akwai wata ƙungiyar wacce tuni tana wannan aikin”.

A don haka a cewarsu, Minista Ngige sam ba shi da hurumin yi wa waɗancan ƙungiyoyi na CONUA da NAMDA rajista. Sun ƙara da cewa, ya kamata ministan ya ƙara fahimtar wancan sashen dokar na 3(2) wanda yake ikirarin shi ya dogara da shi wajen kafa ƙungiyoyin, bayan ƙarara sashen ya haramta masa yi wa wasu ƙunyoyin rajista don wakilta Malaman jami’a a yayin da hukumar ASUU take nan tana cigaba da wanzuwa.

Abin tambayar a cewar su shi ne, shin Ministan ya kuwa girmama waccan dokar? Abinda ya tsaya wa mutane dai a zuciya shi ne, menene manufar Ministan wajen ƙirƙiro waɗannan ƙungiyoyi kuma wanne abu ne yake so ya cimma da wannan lamari.

Sannan sun ƙara tunatar da cewa, ‘yancin tafiya yajin aiki ruwan dare ne gama Duniya, kuma haƙƙin kowacce ƙungiyar kasuwanci ce. Kuma ba a Nijeriya kaɗai ake gudanar da shi ba har ma da ƙasashen da suka cigaba sosai. Ko a ƙasar Ingila kwanan nan ma ƙungiyar ma’aikatan jirgin sama sun yi yajin aikin.

Amma gwamnatin jihar ba ta mai da martani ta hanyar yi wa ƙungiyarsu kishiya ba. Haka a ƙasashen Afirka ma suna yakin amma gwamnati ba ta ɗaukar mataki mai zafi irin haka.

Daga karshe sun ce ya kamata ministan ya sani, ba ƙungiyar da take yin yajin aiki don kawai son ranta. Ko ASUU yajin aikinta ta yi shi ne don ba ta da sauran mafita sai shi ɗin. Amma ba don sun ji daɗin hakan ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *