Adamu ya taya zaɓaɓɓen Gwamnan Ekiti murnar lashe zaɓe

Daga BASHIR ISAH

Shugaban Jam’iyyar APC a ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, sabon zaɓaɓɓen Gwmanan Jihar Ekiti, Mr. Biodun Oyebanji, murnar lashe zaɓen gwamnan jihar da ya gudana a ƙarshen mako.

Adamu ya bayyana a cikin wasiƙar da ya aike wa zaɓaɓɓen Gwamnan cewa, shaharar Oyebanji da kuma himmar da APC ta bayar yayin yaƙin neman zaɓen su ne suka bai wa sabon gwamnan nasarar da ya samu a zaɓen.

Adamu ya ce zaɓaɓɓen Gwamnan a da ƙwarewar da kuma hangen nesan da zai ciyar da Jihar Ekiti gaba

Daga nan, ya yi amfani da wannan dama wajen godiya ga al’umar Jihar Ekiti na mara wa APC ya zuwa cimma wannan nasarar, tare da yi musu alƙawarin sabon Gwamnan zai duba ya ɗora daga inda Gwamna mai barin gado ya tsaya wajen yi wa jihar hidima.

Mr Oyebanji ya lashe zaɓen ne bayan da ya samu ƙuri’a 187,057, inda ya kayar da abokan hamayyarsa Segun Oni na SDP da Bisi Kolawole na PDP da sauransu.

Jam’iyyar SDP ce ta zo ta biyu a zaɓen da ƙuri’u 82,211, yayin da PDP ta zo ta uku da ƙuri’u 67,457.

Ya zuwa watan Oktoba mai zuwa ake sa ran za a rantsar da Mr Oyebanji a matsayin sabon gwamnan Ekiti don ya gaji mai barin gado Kayode Fayemi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *