Akume ya ƙalubalanci masu gidajen caca kan tara wa gwamnati kuɗaɗen shiga

Daga WAKILINMU

Ministan Ayyuka na Musamman, Sanata George Akume, ya buƙaci Hukumar Kula da Harkokin Caca ta Ƙasa (NRLC) da ta ƙara himma wajen tara wa gwamnati kuɗaɗen shiga domin ƙarfafa mata wajen yi wa ƙasa ayyukan cigaba da inganta tattalin arziki.

Akume ya buƙaci hakan daga hukumar ne a Alhamis da ta gabata yayin wata ganawa da masu ruwa da tsaki a masana’antar caca a Abuja. Inda ya ce an rigaya an bai wa hukumar dama don yin abin da ya kamata.

Ya ce, “Abin takaici ne ganin yadda ake tafka hasarar ta wannan ɓangare saboda babu abin da ke shigowa aljihun gwamnati.”

Ya ƙara da cewa, “Abin damuwa ne ganin yadda wasu mambobin harkar ba su halarci taron ba. Wannan abu ne da ba za a bari ya ci gaba da faruwa ba saboda babu wanda ya fi hukuma, don haka ba za a lamunci halin rashin daraja gwamnati ba.

“Shekaru da dama mun yi ta buƙatar a samar da wani tsarin bai ɗaya na sanya wa masana’antar ido, yanzu tun da an samu tsarin lamurra ba za su ci gaba da tafiya a haka ba, dole ne mu ci gaba.

“Na yi ta ƙoƙarin ganin cewa harkar caca ta inganta kamar yadda lamarin yake a ƙasashen duniya. Galibin masu gidajen cacar ba su sauke haƙƙoƙin da suka rataya a kansu ga hukumar.”

A nasa ɓangaren, shugaban hukumar, Lanre Gbajabiamila, ya ce a sane yake da irin ƙalubalen da masu gidajen caca ke fuskanta, tare da bada tabbacin hukumar za ta yi bakin ƙoƙarinta wajen magance musu matsalolinsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *