An gudanar da zanga-zangar ƙin amincewa da dakatar da Gudaji Kazaure daga APC

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Ɗaruruwan ‘yan jam’iyar APC da magoya bayan xan majalisar tarayya mai wakiltar al’ummar ƙananan hukumomin Kazaure, Roni, Gwiwa da ‘Yankwashi, Hon. Muhammad Gudaji Kazaure ne suka gudanar da zanga-zangar ƙin amincewa da dakatar da wakilin nasu da jam’iyyar APC ta yi.

Masu zanga-zangar sun zargi gwamnan jihar Jigawa, Mohammed Badaru Abubakar da ɗaukar matakin ɗauki ɗora da ya yi wa mafi yawancin al’ummar ƙananan hukumomin jihar, inda ya zaɓi mutanen da za su yi wa jam’iyar APC takarar shugabancin ba tare da tuntuɓar masu ruwa da tsaki a ƙananan hukumomin ba.

Matasan wanda suke ɗauke da kwalaye masu rubutu mabambanta: ‘Gudaji wakili ne nagari mai hidimtawa al’ummar sa’, ‘Gudaji mutumin mutane ne, mai ƙaunar talaka’ da sauran su.

Sun gudanar da zanga-zangar cikin lumana inda suka tashi daga Kanti zuwa cikin gari fadar Mai Martaba Sarkin Kazaure, amma jami’an tsaro sun hana su ƙarasawa zuwa fada don shigar da ƙorafin su ga uban ƙasa.

Shugaban matasan na jam’iyyar APC a ƙaramar hukumar Kazaure, Bilyaminu Lawan yana daga cikin waɗanda suka karɓi masu gudanar da zanga-zangar, ya kuma tabbatar masu za su kai ƙorafin su ga uwar jam’iyyar ta kasa domin samun maslaha.

Bincike ya tabbatar da matakin da Gwamna Badaru ya ɗauka bai yi wa mafi yawancin zaɓaɓɓu da masu riƙe da muƙamin siyasa da sauran al’ummar daɗi ba, ganin yadda wanda suka yi masa hidima a zaɓen 2015 da 2019 ba a tuntuve su ba wajen fitar da ‘yan takarar shugabancin ƙananan hukumomin.

Sakamakon hakan ne ɗan majalisar tarayya, Gudaji Kazaure ya bayyana rashin gamsuwar sa tare da bada shawarar da a gaggauta yin gyara don ciyar da jam’iyyar APC gaba musamman bisa la’akari da zaɓen 2023 mai cike da ruɗani.

Wannan ya sa shugaban ƙaramar hukumar Kazaure, Hon. Jamilu Zaki tare da haɗin gwiwar wasu mutane uku suka rattava wa wata takarda hannu tare da sanar da dakatar da Hon. Gudaji Kazaure daga Jam’iyyar APC reshen ƙaramar hukumar Kazaure.

Fitowar takardar ke da wuya sai Hon. Gudaji Kazaure ya maida martani inda ya bayyana dakatarwar da aka yi masa a matsayin wasan yara da kuma wani yunquri na vata masa suna, inda ya ce yana nan a jam’iyyar APC kuma mutum huɗu ba za su iya yanke hukunci ba.