An sako ɗaya daga cikin ɗaliban jami’ar da aka yi garkuwa da su a Kaduna

Daga AISHA ASAS

‘Yan bindiga sun sako ɗaya daga cikin ɗaliban jami’ar Greenfield da suka yi garkuwa da su kwanan nan a Kaduna.

Kodayake dai babu wani bayani a hukumance da ya tabbatar da hakan, amma mahaifiyar ɗalibin da ya kuɓutan, Lauritta Attahiru ta tabbatar wa manema labarai kan cewa ɗanta ya dawo gida.

Sai dai Lauritta ba ta yi cikakken bayani ba dangane da yadda aka yi ɗan nata ya dawo gida ba, sai da aka biya fansa ko kuwa a’a.

Wata majiya ta faɗa cewa a ranar Asabar da ta gabata aka sako ɗalibin bayan kuma mahaifiyarsa ta biya kuɗin fansa a ɓoye.

Iyayen yaran da lamarin ya shafa sun ce da farko ɓarayin sun buƙaci da su biya Naira N20 a kan kowane ɗalibi kafin a sake shi, amma daga bisani sai suka dawo suka ce a haɗa musu milyan N100 da babura guda 10 kafin su sako ɗaliban.

Iyayen sun yi kira ga gwamnati da ma al’ummar ƙasa baki ɗaya da a kawo musu ɗauki kan wannan bala’i da ya same su domin a samu ‘ya’yansu su dawo gare au lami lafiya.

Yanzu haka dai ɗalibai su 16 ne suka rage a hannun ‘yan fashin, kuma sun yi barazanar hallaka baki ɗayansu muddin iyayensu da gwamnati suka gaza samar da kuɗaɗe da baburan da suka buƙaci a ba su.