Ana fargabar mutum da dama sun mutu a hatsarin jirgin ƙasa da mota a Legas

Dag BASHIR ISAH

Ana fargabar mutanen da ba a tantance adadinsu ba sun mutu, sannan da dama sun jikkata sakamakon hatsarin da ya auku tsakanin jirgin ƙasa da wata mota bas (BRT) da safiyar Alhamis a Legas.

Wani mai amfani da kafar Tiwita, @Trutfully83, shi ne ya bayyana hakan a shafinsa.

Inda ya wallafa cewar “an samu aukuwar hatsari motar BRT mai ɗauke da fasinjoji da kuma jirgin ƙasa a yankin Ikeja a Legas.

“Ba a tantance adadin waɗanda suka mutu ba a wannan lokaci, amma waɗanda hatsarin ya rutsa da su ɗin na buƙatar kulawar gaggawa,” in ji shi.

Kalli bidiyon hatsarin: