APC a Kano ta buƙaci mambobinta su kwantar da hankalinsu

Daga RABI’U SANUSI a Kano.

Jam’iyyar APC reshen jihar kano ta yi kira ga ‘ya’yanta su da su zama masu kara haƙuri bisa irin ta’asar da magoya bayan jam’iyyar NNPP ke yi masu da sunan murnar lashe zaɓen gwamna da ya gabata a jihar wanda ya saɓa wa doka.

Wannan na zuwa ne a wata sanarwa da Kwamishinan yaɗa labarai kuma kakakin yaƙin neman zaɓen Gawuna da Garo a jihar, Malam Muhammad Garba.

Sanarwar ta ce tana tabbatar wa da jama’ar jihar cewa babu abin da gwamnatin Dr Abdullahi Ganduje ke yi da ya wuce ganin ta samar wa al’ummarta cikakken zaman lafiya da kare dukiyarsu a faɗin jihar.

Ya ƙara da cewa jam’iyyar APC na hattara da yadda aka bayyana sakamakon zaɓe yake tafiya ta ɗauki wannan mataki cikin lokacin da ya dace.

Daga ƙarshe, Muhammad Garba ya kuma buƙaci mambobin APC a jihar da su ci gaba da nuna haƙuri tare da goyon bayansu ga jam’iyyar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *