Atiku zai cefanar da komai na Nijeriya ga ‘yan kasuwa, ka da ku zaɓe shi – Gargaɗin Tinubu ga ‘ya Nijeriya

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

“Atiku…baya son gina kasa mai inganci a maimakon haka zai gwammace ya sayar da hakin ku na haihuwa ga manyan magina,” in ji Mista Tinubu.

Ɗan takarar Shugaban Ƙasa a Jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, ya sake caccakar Atiku Abubakar, yana mai cewa ɗan takarar Jam’iyyar PDP ba zai iya zama Shugaban Nijeriya ba.

Tinubu, wanda ya yi magana a taron yaqin neman zaɓen Shugaban Ƙasa na Jam’iyyar APC a Ondo, ya ce tsohon mataimakin shugaban ƙasar zai sayar da Nijeriya ga ‘yan kasuwa mafi girma idan an bar shi ya yi mulki.

“Atiku Abubakar ba zai iya ba, ba ya son gina al’umma ta gari, a maimakon haka ya gwammace ya sayar da haƙƙin ku na haihuwa ga manyan ‘yan kasuwa. Manufofin Atiku da aiki ba komai ba ne,” inji shi a taron gangamin da aka yi ranar Asabar a Akure.

Tinubu da Atiku Abubakar za su haɗu da sauran ‘yan takarar shugaban ƙasa da suka haɗa da Peter Obi na LP da Rabiu Kwakwanso na NNPP a zaɓen.

‘Yan takarar dai za su fafata ne domin karɓar ragamar mulki daga hannun Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, wanda zai kammala wa’adin mulkinsa na tsawon shekaru takwas a ranar 29 ga watan Mayu.

Ko da yake Atiku Abubakar yana fuskantar turjiya a cikin gida daga jam’iyyarsa tun bayan da ya zama ɗan takarar shugaban ƙasa a Jam’iyyar PDP.

Bayyanar sa da kuma zaɓen gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa a matsayin mataimakinsa, ya fusata wasu gwamnonin ƙarƙashin jagorancin Nyesome Wike na Jihar Ribas.

Gwamnonin G5, da suka haɗa da Wike, Samuel Ortom (Benuwai), Okezie Ikpeazu (Abia), Ifeanyi Ugwuanyi (Enugu), da Seyi Makinde (Oyo), sun sha cewa ba za su goyi bayan takarar Atiku Abubakar ba, kuma sun ci gaba da nesanta kansu daga yaƙin neman zaɓensa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *