14
Nov
Daga BASHIR ISAH Wata ƙungiya ta mabobin Jam'iyyar ANPP tare da tawagar masu ruwa da tsaki sun buƙaci 'yan Nijeriya da su bai wa Shugaba Bola Ahmad Tinubu da gwamnatinsa cikakken goyon baya don cigaban ƙasa. Ƙungiyar ta buƙaci hakan ne cikin sanarwar da ta fitar a Abuja mai ɗauke da sa-hannun shugabanta, Malam Kabiru Muhammad Gwangwazo. Da yake tsokaci kan nasarar da Tinubu ya samu a Kotun Ƙoli, Muhammad wanda tsohon shugaban ANPP ne a Jihar Kano, ya yi kira ga ɗaukacin masu ruwa da tsaki da su rufa wa Tinubu da gwamnatinsa baya don amfanin ƙasa. Ya ce,…
