Editor

9513 Posts
‘Yan bindiga sun kashe mutum tara tare da yin awon gaba da wasu da dama a Katsina

‘Yan bindiga sun kashe mutum tara tare da yin awon gaba da wasu da dama a Katsina

Daga UMAR GARBA a Katsina Wasu mahara ɗauke da muggan makamai da ake kyautata zaton ɓarayin daji ne sun hallaka mutum tara, gami da yin garkuwa da wasu mutane da dama a qaramar hukumar ɗan Musa da ke jihar Katsina. Wani mazaunin garin da aka sakaya sunansa, ya bayyana wa MANHAJA cewa maharan waɗanda ba zai iya ƙiyasta yawansu ba, sun afka wa garin cikin daren ranar Lahadi da misalin ƙarfe 8:00 na dare. A cikin mutane tara da suka rasa rayukansu sakamakon harin, har da ɗan sanda da kuma tsohon kantoma na ƙaramar hukumar, wato Hon. Dauda Lawal Mai…
Read More
‘Yan sanda sun cafke babban wanda ake zargi da kashe matar aure a Borno

‘Yan sanda sun cafke babban wanda ake zargi da kashe matar aure a Borno

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Rundunar 'yan sanda a jihar Borno, a ranar Talata ta ce ta saki mijin matar da aka kashe a gidan aurenta da ke Maiduguri bayan ta kama babban wanda ake zargi. Rundunar 'yan sandan ta ce an sako mijin marigayiyar, mai suna Adamu Ibrahim da abokinsa, Bukar Wadiya da aka tsare su bayan sun kai rahoton afkuwar kisan ga 'yan sanda. Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar ta hannun mai magana da yawunta ASP Sani Kamilu. Ya ce an bi sawun babban wanda ake zargin, Abacha Bukar tare da…
Read More
Ministan Labarai ya buƙaci ‘yan Nijeriya su mara wa burin Tinubu baya don farfaɗo da ƙasa

Ministan Labarai ya buƙaci ‘yan Nijeriya su mara wa burin Tinubu baya don farfaɗo da ƙasa

Daga BASHIR ISAH Ministan Labarai da Wayar da Kan 'Yan Ƙasa, Mohammed Idris, ya ce tun da yanzu Kotun Ƙoli ta yanke hukunci, kamata ya yi 'yan ƙasa a haɗe kai sannan a mara wa burin farfaɗo da ƙasa da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ke da shi. Ministan ya bayyana haka ne yayin taron manema labarai a Abuja biyo bayan hukuncin Kotun Ƙoli na tabbatar da nasarar da Shugaba Tinubu ya samu a babban zaɓen 2023. Ya ce shari'a ta wuce, yanzu lokaci ne da ɗaukacin 'yan Nijeriya za su haɗa kai wajen ciyar da ƙasa gaba. Ya ce tun…
Read More
Da Ɗumi-ɗumi: Sarkin Ƙasar Ebira, Ado Ibrahim ya kwanta dama yana da shekara 94

Da Ɗumi-ɗumi: Sarkin Ƙasar Ebira, Ado Ibrahim ya kwanta dama yana da shekara 94

Daga BASHIR ISAH Allah Ya yi wa Sarkin Ƙasar Ebira (Ohinoyi of Ebiraland), Dokta Ado Ibrahim, rasuwa. MANHAJA ta tattaro cewar Basaraken ya rasu ne da safiyar Lahadi, inda ya bar duniya yana da shekara 94. Majiyarmu ta ce marigayin ya rasu ne a wani asibitin Abuja inda yake jinya. Majiyar ta ce za a yi jana'izar marigayin a wannan Lahadin a Okene babbar cibiyar Masrautar Ebira a Jihar Kogi. An haifi marigayin ne a ranar 7 ga Fabrairun 1929, kuma ya zama sarki ne a ranar 2 ga Yunin 1997.
Read More
Mun samu ƙorafe-ƙorafe masu yawa a Kano kan take haƙƙin ɗan Adam – Shehu Abullahi

Mun samu ƙorafe-ƙorafe masu yawa a Kano kan take haƙƙin ɗan Adam – Shehu Abullahi

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano Hukumar Kare Haƙƙin ɗan Adam ta Ƙasa reshen Jihar Kano ta samu ƙorafe-ƙorafe da yawa a ɓangarori daban-daban na take haƙƙin ɗan Adam. Shugaban hukumar Alhaji Shehu Abullahi ne ya bayyana hakan da yake zantawa da 'yan jarida, ya ce ƙorafin ya fi shafar mata da ƙananan yara domin kuwa a wannan shekarar daga watan uku zuwa watan Oktoba sun samu ƙorafe-ƙorafe guda 1'147. Ya qara da cewa daga cikin wannan adadi ofishinsa ya yi ƙoƙarin kammala ayyuka akan guda 1,320 sannan akwai guda 227 suna cigaba da yin ayyuka a kansu. Shugaban na hukumar…
Read More
Fidelity Bank ya maido da zarafin tura kuɗi zuwa bankunan OPay, Kuda, Moniepoint da Palmpay

Fidelity Bank ya maido da zarafin tura kuɗi zuwa bankunan OPay, Kuda, Moniepoint da Palmpay

Daga BASHIR ISAH Bankin Fidelity ya maido da zarafin yin tiransifa ta yadda a yanzu kostomominsa za su iya ci caba da tura kuɗi zuwa bankuna irin su OPay da Moniepoint da Palmpay da kuma Kuda. Wannan na zuwa bayan da a 'yan makonnin da suka gabata Bankin Fidelity ya daƙile damar yin tiransifa zuwa wasu bankuna saboda yawaitar harkokin 'yan damfara da kuma tantance kostomominsa. Majiya daga bankin ta ce yanzu bankin ya buɗe hanyar ci gaba da tiransifa ta yadda a abokan mu'amalarsa za su ci gaba da tura kuɗi zuwa bankunan da a baya ya katse zarafin…
Read More
Matsalar matsananciyar yunwa a Nijeriya

Matsalar matsananciyar yunwa a Nijeriya

An yi hasashen cewa 'yan Nijeriya miliyan 25 na iya fuskantar matsananciyar yunwa tsakanin watan Yuni zuwa Agusta 2023 (lokacin bazara) idan ba a ɗauki matakan gaggawa ba don magance matsalar. Asusun kula da ƙananan yara na Majalisar Ɗinkin Duniya (UNICEF) ya nakalto Cadre Harmonise a watan Oktoba na shekarar 2022, wani bincike na abinci mai gina jiki ƙarƙashin jagorancin gwamnati da Majalisar Ɗinkin Duniya, yana mai nuni da cewa an yi hasashen cewa alƙaluman na ƙaruwa daga sama da mutane miliyan 17 da ke fuskantar barazanar ƙarancin abinci a halin yanzu a Ƙasar. A cikin wannan adadi, mutane miliyan…
Read More
Zambo cikin aminci: Waƙoƙin Rarara a siyasar Kano

Zambo cikin aminci: Waƙoƙin Rarara a siyasar Kano

Daga FARFESA ABDALLA UBA ADAMU Fassara: HASSAN AUWALU MUHAMMAD A cikin shekaru 43 da suka gabata da na kasance mai bincike, akwai ɓangarori biyu da na ƙi karkatar da aikin bincikena akai: siyasa da addini. Idan kun ga hannuna a cikin ɗayan waɗannan biyun, wajen da na shahara ne, wato kan al'adun yaɗa labarai. Misali, da na yi rubuce-rubuce da yawa na Zikirin Anfasu na ‘yan Ƙadiriyya, ba na yi a matsayin ɗaya daga cikin mabiyan ɗariqar ba, sai dai a matsayina na mai binciken harkar kiɗe-kiɗe - na mai da hankali kan yadda suke dukan jikinsu tare da motsa…
Read More
Jam’iyyar APC ba ta da ɗan takarar Gwamna a Jihar Bayelsa – INEC

Jam’iyyar APC ba ta da ɗan takarar Gwamna a Jihar Bayelsa – INEC

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa INEC, ta fitar da sunayen ‘yan takarar gwamnan Bayelsa da Imo da aka yi wa gyaran fuska. Bisa ga lissafin da aka yi wa gyaran fuska da hukumar ta wallafa a ranar Talata, ba a saka sunayen Timipre Sylva da abokin takararsa, Joshua Maciver na jam’iyyar All Progressives Congress ba a zɓen jihar Bayelsa. Sakatariyar Hukumar, Rose Oriaran-Anthony ne ta sanya hannu a jerin sunayen. Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya ya bayar da rahoton cewa, an bar shafi na sunayen ɗan takarar Jam’iyyar APC da abokin takararsa tare…
Read More
Jam’iyyar APC a Taraba ta koka kan ƙin bai wa Mustapha muƙami a gwamnatin Tinubu

Jam’iyyar APC a Taraba ta koka kan ƙin bai wa Mustapha muƙami a gwamnatin Tinubu

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Jam’iyyar APC reshen Jihar Taraba ta yi Allah-wadai da rashin shigar da tsohon Sakatare kuma mai bada shawara kan harkokin shari’a na Ƙungiyar Yaƙin Neman Zaven Tinubu/Shettima a jihar Mohammed Mustapha a cikin majalisar ministocin Shugaba Bola Tinubu. A cikin wata sanarwa da Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙaramar Hukumar Jalingo kuma shugaban ƙungiyar 16 Ciyamomi (ALGON), Bashir Bakari da wakilan shugabannin gundomomi Hon. Bello Hassan, sun bayyana damuwar su cewa ba a ɗauki Mustapha ko a saka shi a matsayin minista ba ko ba shi wani muƙami a gwamnatin TinubuSanarwar ta ci gaba da…
Read More