28
Oct
Daga JAMIL GULA a Kebbi 'Yan kasuwa da ke hada-hada kan hanyar garin Bachaka da ke kan iyakokin Nijeriya da Jamhuriyar Nijar a ɓangaren Jihar Kebbi sun koka bisa yadda jami'an tsaro suka mayar da su waɗansu shanun tatsa. Alhaji Umar Ɗankirya ɗaya daga cikin shugabannin 'yan kasuwa da ke sayar da abinci ne ya bayyana haka a wata zantawa da wakilinmu a garin Bachaka ƙarshen makon da ya gabata. Alhaji Umar ya ce jami'an tsaro da suka haɗa da 'yan sanda da masu hana fasakwabri da jami'an shige da fice da na farin kaya da ke aiki kan wannan…
