Editor

9513 Posts
Kamfanonin MTN da Airtel sun samu lasisin gudanar aikin banki

Kamfanonin MTN da Airtel sun samu lasisin gudanar aikin banki

Daga AMINA YUSUF ALI Manyan kamfanonin sadarwar nan na MTN da Airtel sun samu lasisin tafiyar da harkokin banki da hada-hadar kuɗi a Nijeriya. Shi dai kamfanin MTN, wanda ya mamaye kaso 40 na kasuwar sadarwa a ƙasar, da kuma Airtel, wanda ya mamaye kaso 27, sun samu sahalewar Babban Bankin Nijeriya (CBN), domin su fara tafiyar da harkokin banki a faɗin ƙasar, kamar yadda jiga-jigan  kamfanonin sadarwar guda biyu suka bayyana a ranar Juma'ar da ta gabata.  Kamfanonin sun bayyana hakan a wasu takardu mabanbanta da kamfanonin sadarwar suka aike wa da hukumar canji ta ƙasar Nijeriya.  Shi dai…
Read More
Rushewar benaye da ban tsoro

Rushewar benaye da ban tsoro

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA A Babban Birnin Tarayyar Nijeriya, Abuja, ko a Legas da ke bakin teku babu inda ba a tava samun aukuwar rugujewar bene ba, kuma duk lokacin da irin wannan akasi ya auku sai an samu asarar rayuka. Wani lokacin za ka tarar mutanen da akasin ya rutsa da su na zaune ne a cikin benen da ba a kammala ba sai ya ruguje a kansu, inda a wani lokacin kuma ma'aikatan da ke aikin ginin ne hakan kan rutsa da su. Na baya-bayan nan shi ne wanda ya faru a Ikoyi da ke Jihar Legas, inda…
Read More
Batun ayyukan madatsun ruwa da aka watsar

Batun ayyukan madatsun ruwa da aka watsar

Ga duk al’ummar da ta ke da muradin mayar da noma wani ginshiƙin tattalin arzikinta, sanin cewa an yi watsi da ayyukan ruwa ko madatsun ruwa kusan 400 abu ne mai matuƙar tayar da hankali. Shugaban kwamitin majalisar dattijan Nijeriya mai kula da albarkatun ruwa, Sanata Bello Mandiya, ne ya bayyana hakan a ranar Talata yayin da ya ke zantawa da manema labarai bayan kammala zaman kare kasafin kuɗi da suka yi da ministan albarkatun ruwa, Injiniya Suleiman Adamu, inda ya koka da cewa da yawa daga cikin madatsun ruwa ba su da wani amfani a ƙasar. Sanata Mandiya ya…
Read More
Nijeriya ta jaddada sadaukarwa ga yarjejeniyar magance bala’o’i ta Sendai a taron COP26

Nijeriya ta jaddada sadaukarwa ga yarjejeniyar magance bala’o’i ta Sendai a taron COP26

Daga WAKILINMU Gwamnatin Tarayya ta nanata ƙudirin ta na aiwatar da tsarin rage aukuwar bala'o'i wanda aka yi a Sendai domin aiwatarwa daga 2015-2021. Ministar Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa, Hajiya Sadiya Umar Farouq, ita ce ta bayyana haka a lokacin da ake tattaunawa kan tsarin da Nijeriya ta ke bi wajen amfani da sauyin yanayi don rage aukuwar bala'o'i a taron duniya kan sauyin yanayi, wato COP26, wanda aka yi a ranar Litinin a birnin Glasgow na ƙasar Sukotland. A jawabin da ta gabatar kan ƙoƙarin Nijeriya wajen magance matsalolin rayuwa da sauyawar yanayi ke haifarwa, a wani…
Read More
Matsalar warin baki da hanyoyin magance ta (2)

Matsalar warin baki da hanyoyin magance ta (2)

Daga BILKISU YUSUF ALI Ci gaba daga makon da ya gabata Duk da warin baki ba za a kira shi da gama-garin matsala ba amma mutane da yawa na fama da shi kuma matsala ce da ake iya jin ta daga nesa kafin ma a kusanci mutum. *Babbar matsala ta farko da ke janyo warin baki shi ne rashin tsaftar baki , in kuwa haka ne maganin farko na wannan matsalar shi ne tsaftace baki da duk nau’ikan abin da aka tanada don tsaftace baki. *Ganin likitan haƙori duk lokacin da aka fuskanta akwai matsala ta ciwon haƙori ko dasashi,…
Read More
Adabin Hausawa ba zai manta da Umaru Ɗanjuma ba – Dakta Abu Sabe

Adabin Hausawa ba zai manta da Umaru Ɗanjuma ba – Dakta Abu Sabe

*Mutum ne da kowa ke jin daɗin mu'amala da mahaifina, inji ɗan Marigayi Umaru Ɗanjuma Daga UMAR GARBA a Katsina A ranar juma'a 29 ga watan Oktoba 2021, Allah ya karvi rayuwar shahararren marubucin littattafai kuma ɗaya daga cikin waɗanda su ka fara wasan kwaikwayo a arewacin Nijeriya wato Alhaji Umaru Ɗanjuma Katsina wanda aka fi sani da Kasagi. Marigayi Umaru Ɗanjuma Katsina ya yi fice ta fannin wasannin kwaikwayo kamar su 'magana Jari ce', 'Ruwan Bagaja', 'Kasagi', 'Ya'yan Zamani' da sauran su, ya kuma rubuta littattafai waɗanda su ka zagaya duniya kamar su 'Kulɓa na Ɓarna', 'Ai Ga Irinta…
Read More
Zan yi aiki da kai – Buhari ya taya zaɓaɓɓen gwamnan Anambara murna

Zan yi aiki da kai – Buhari ya taya zaɓaɓɓen gwamnan Anambara murna

Daga BASHIR ISAH Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, ya taya sabon zaɓaɓben gwamnan jihar Anambara, Farfesa Charles Chukwuma Soludo na jam'iyyar APGA, murnar nasarar da ya samu a zaɓen jihar Anambara da ya gudana a ƙarshen makon da ya gabata. Buhari ya taya Soludo murna ne ta hanyar wallafa saƙon a shafinsa na facebook, tare kuma da yaba wa jami'an tsaro bisa ƙoƙarin da suka yi wajen tabbatar da zaɓen ya gudana lami lafiya, da kuma hukuma INEC dangane da nasarar gudanar da zaɓen da ta samu duk da irin tulin ƙalubalen da ta fuskanta. Buhari ya yi amfani da wannan…
Read More
Yarabawa da al’adunsu

Yarabawa da al’adunsu

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Jaridar Manhaja za ta ci gaba da kawo wa masu karatu tarihi na manyan ƙabilun Nijeriya guda huɗu da suka haɗa da Yarabawa, Hausawa, Igbo da kuma Fulani cikin mako huɗu a jere. Ƙasar Yarabawa wani yanki ce na duniya da ake samu a bigiren 6o da 9o na Arewacin Latitu (Latitude North) sannan kuma tana bigire na 2o30’ da kuma 6o30’ ta Gabas da Longitu (Longitude East). Tana iyaka da Jihar Neja (Niger State) daga Yamma Maso Arewa. Ta Gabas kuma tana iyaka da ƙasar Jamhuriyar Bini; wato Kwatano (Benin Republic). Sai kuma Tekun Atilantika…
Read More