Editor

9513 Posts
Ina zubar da hawaye idan na tuna matsalolin da na fuskanta a gidan aure – Hajaru Sanda

Ina zubar da hawaye idan na tuna matsalolin da na fuskanta a gidan aure – Hajaru Sanda

“Mata ma 'ya'ya ne, ku ba su damar karatun boko kamar maza” Daga AMINU AMANAWA, a Sokoto Ba wa mata damar shiga makarantu domin neman ilimi boko kusan wani ƙalubale ne da aka daɗe ana fama da shi a Ƙasar Hausa. Da yawa akwai masu kallon bawa mata damar neman ilimin boko a matsayin lamarin da bai dace ba, bisa wasu hujjojin da suka kaɗai suka sani. Hajaru Aliyu Sanda, fitacciya a fagen gwagwarmayar kare haƙƙin bil'adama, 'yar siyasa ce, kana kuma ‘yar kasuwa. Ta bayyanawa wakilin mu a Sokoto Aminu Amanawa, irin ƙalubalen da ta fuskanta kafin kaiwa matakin…
Read More
Numfashin mutum

Numfashin mutum

Daga MUSTAPHA IBRAHIM ABDULLAHI ’Yan uwa masu karatu, assalam aliakum. Barkanmu da wannan lokaci, barkan mu da sake saduwa a wannan shafi mai albarka da ke kawo muku bayanai game da jikin ɗan Adam, domin ku fa’idantu, kusan yadda jikin ku ke aiki. Rubutun yau zai mayar da hankali kan wani babban al'amari da ɗan Adam ke yi kulla- yaumin ba tare da ya kula da shi ba. Ku dai kawai ku biyo ni.  Jiki na da naka, da naki, yana gudanar da al’amuran yau da kullum masu tarin yawa, waɗanda da zamu zauna domin mu ƙididdige su, sai dai…
Read More
INEC ta bayyana Soludo a matsayin wanda ya lashe zaɓen Anambara

INEC ta bayyana Soludo a matsayin wanda ya lashe zaɓen Anambara

Daga BASHIR ISAH Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta bayyana Farfesa Chukwuma Soludo na jami'iyyar APGA a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar Anambara da aka gudanar ran 6 ga Nuwamba. Bayan ƙidayar ƙuri'u, INEC ta ce ƙuri'u 112,229 Soludo ya samu wanda hakan ya ba shi nasara a kan ɗan takar PDP, Mr Valentine Ozigbo wanda ya samu ƙuri'u 53, 807, wato shi ne dan takara na biyu mai mafi yawan ƙuri'u. Sai kuma ɗan takarar APC,Sanata Andy Uba da ya zo na uku da ƙuri'u 43,285. Malamar zaɓen, wato Farfesa Florence Obi, ita ce ta bayyana wannan…
Read More
Saura ƙiris a bai wa hamata iska a tskanin jami’an gwamnati kan Abdulrasheed Maina

Saura ƙiris a bai wa hamata iska a tskanin jami’an gwamnati kan Abdulrasheed Maina

Daga BASHIR ISAH An samu 'yar ƙwarya-ƙwaryar wasan kwaikwayo a harabar Babbar Kotun Abuja tsakanin jami'an kula da gidan yari da na EFCC bayan da kotun ta yanke wa tsohon shugaban kwamitin yi wa fansho garambawul ko kuma PRTT a taƙaice, Abdulrasheed Maina hukuncin zaman gidan yari na shekaru takwas. Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya ya ruwaito cewa, Alƙali Okon Abang shi ne wanda ya yanke hukuncin ingiza ƙeyar Maina zuwa gidan yari bayan da hukumar EFCC ta maka shi a kotu bisa tuhumar badaƙalar kuɗaɗe. Alƙali Abang ya bada umarnin Maina zai soma zaman kurku na duka laifuka 12…
Read More
WASIƘU: Shawarwari ga matasa masu shirin aure (2)

WASIƘU: Shawarwari ga matasa masu shirin aure (2)

Assalamu alaikum, kamar yadda muka faɗa a makon da ya gabata cewa, za mu cigaba daga inda muka tsaya. Abu na biyu da zan gaya muku shi ne yana da kyau ku fahimci cewa waɗannan abubuwa ba a samunsu haka kawai, wato ba sa samun mutum haka kawai, dole ne ku yi ƙoƙari wajen samar da su. Hanyar samar da su kuwa ita ce dukkan ma'auratan su so junansu. Wataƙila ku tambaya ta ya ya? Kamar yadda ake cewa ne, "ba a iya tabbatar da so da ƙauna ta hanyar ƙarfi da tursasawa", lalle haka ne don kuwa so kamar…
Read More
An rantsar da shugaban ƙungiyar GDF

An rantsar da shugaban ƙungiyar GDF

Daga MUHAMMAD MUJITABA A cikin makon nan ne aka rantsar da shugabanin haɗaɗiyar ƙungiyar cigaban unguwar gwammaja da ke Dala ta Jihar Kano watou ‘Gwammaja Development Forum’ ƙarƙashi shugabancin Abdulshakur Tahir, a matsayin babban shugaban GDF na farko. Shugabanin da aka zaɓa kuma aka rantsar da su ne Sani Usman, mataimakin shugaba, Fatihu Sani Imam Sakatare, Baffa Ismail, mataimakin sakatare, Abba Rabiu Ali, Sakataren kuɗi, Mujittafa Ismail, ma’ajin kuɗi, sauran dai su ne akwai Mustapha Abdullahi a matsayin jami’in hulɗa da jama’a, Fatihu Ashiru Lawan, Jamil hulɗa da jama’a na biyu, jami’in kula da jin daɗi  ’yan qungiyar GDF shi ne…
Read More
Shugaban ƙungiyar Fitiyanul Islam ya yaba da maulidin Ma’ahad Wailari

Shugaban ƙungiyar Fitiyanul Islam ya yaba da maulidin Ma’ahad Wailari

Daga MUHAMMAD MUJITABA Sheikh Malam Tujjani Mai Salati Indabawa na daga cikin manya baƙi da suka halarci gagarimin taron Maulidi na makarantar Islamiyya mai suna Ma’ahad Sayyidina Usman Litahafizul Ƙur’an a karo na shida da ke unguwar wailari cikin ƙaramar hukumar Kumbotso Jihar Kano, wanda ya gabata a ranar Lahadi ta gabata a harabar makarantar. Haka kuma ya nuna farin ciki da wannan maulidi wanda ya nuna da cewa abu ne mai falala a duniyarmu da lahirarmu. Kamar dai yadda malam Tujjani Mai Salati Shugaban Fitiyanu Islam ya nuna haka. Shi ma a jawabin sa shugaban makarantar a Ma’ahad, Malam…
Read More
Ƙungiyar Raudha ta yi bikin bayar da kyaututtuka a Kano

Ƙungiyar Raudha ta yi bikin bayar da kyaututtuka a Kano

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Ƙungiyar Raudhatu-Rasul Ayagi ta yi bikin bayar da kyaututtuka ga zakarun musabaƙar yabon Annabi Muhammad (SAW). Taron wanda shi ne karon na farko ya gudana ne a unguwar Gwauron Dutse, makarantar Hajara Buhari cikin birnin Kano. Bilyaminu Zakariyya Ayagi (Abulwarakat) shi ne shugaban ƙungiyar Raudha ya ce, sun shirya taron ne don zaburar da matasa yadda za a tsabtace yabon ma’aiki (SAW). Mai martaba sarkin Kano, Alhaji Aminu Bayero ya ce, ya yabawa wannan ƙungiya inda ya ce, "muna alfahari da samuwar irin wannan ƙungiyoyi da matasan cikin al'ummarmu ke yi don yadawa da qara…
Read More
Ƙungiyar GSK ta kashe miliyan N50 a cibiyoyin kiwon lafiya na Jigawa

Ƙungiyar GSK ta kashe miliyan N50 a cibiyoyin kiwon lafiya na Jigawa

Daga UMAR AƘILU MAJERI a Dutse Wata ƙungiya mai rajin kare lafiyar ƙananan yara tare da haɗin gwiwar GSK ƙarkashin shirin yaƙi da cutar nimoniya sun samar da tallafin kayayyakin kiwon lafiya da magunguna wanda kuɗin su ya kai aƙalla naira miliyan 50 a cibiyoyin lafiya guda 35 a Jihar Jigawa. Shugaban shirin yaƙi da cutar nimoniya, Dakta Adamu Isah ya bayyana hakan a lokacin da ya ke miƙa kayayyakin tallafin ga Gwamnatin Jihar jigawa wanda aka gudanar a ofishin ƙungiyar ceto ƙananan yara da ke Dutse. A cewarsa, sun samar da kayayyakin tallafin ne bayan nazarin da suka yi…
Read More