09
Nov
Daga JOHN D. WADA a Lafiya An buƙaci mata musamman matan Musulmi da su ke yankin Ƙaramar Hukumar Keffi na Jihar Nasarawa da ma ƙasar baki ɗaya da su ci gaba da riƙe ibada da amanar aurensu a duk inda suka tsinci kansu a kuma kowanna lokaci. Shugabar ƙungiyar matan musulmi da aka fi sani da ‘Matan Da’awa’ ta ƙasa reshen Jihar Nasarawa, Malama Aisha Ibrahim ce ta yi wannan kira a lokacin da ta ke zantawa da wakilinmu a garin Keffi hedikwatar ƙaramar hukumar Keffi a Jihar Nasarawa. Ta ƙara da cewa, kiran ya zama wajibi idan aka yi…
