13
Aug
Bayan kwanaki biyar da yin garkuwa da shi, 'yan bindiga sun sako Kwamishinan Yaɗa Labarai na Jihar Neja, Alhaji Sani Idris, da suka sace a jihar. Sanarwar da ta fito daga ahalin kwamishinan, ta nuna an sako Idris ne da misalin ƙarfe 9:30 na dare ran Alhamis da ta gabata. Mr. Ado Ada, wanda ɗan'uwa ne ga kwamishinan, ya bayyana farin cikinsu dangane da dawowar Idris, tare da danganta nasarar dawowar da ƙoƙarin 'yan'uwansa ba tare da biyan wani kuɗin fansa ba. Sanarwar ta ce bayan da aka sako Idris, sai da aka binciki lafiyarsa kana daga bisani aka miƙa…
