13
Aug
13
Aug
Gwamnan Jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya yi tir da yadda ake samun aukuwar yadda jami'an Hukumar Kwastam ke kashe 'yan jihar saboda tuƙin ganganci da abubuwan hawa. Gwamnan ya bayyana ɓacin ransa ne cikin wata sanarwa wadda Darakta Janar na Yaɗa Labaran Gwamnatin Jihar, Abdu Labaran Malumfashi, ya sanya wa hannu a ranar Juma'a. Masari ya ce, daga wannan lokaci gwamnatinsa ba za sake lamuntar aukuwar irin haka a jihar ba. Gwamnan ya yi magana ne a matsayin martani dangane da mummunan haɗarin da ya auku a Litinin da ta gabata a jihar, inda wani jami'in Kwastam ya murƙushe…
13
Aug
Ranar 25 ga Satumba mai zuwa Sarkin Argungu a jihar Kebbi, Alhaji Mohammed Mera, zai naɗa Ministan Yaɗa Labarai da Al'adu, Alhaji Lai Mohammed, a matsayin Kakakin Kebbi. Bayanin hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) ya samu a ranar Juma'a. A bara ne Sarkin Argungu ya sanar da naɗa Lai a muƙamin yayin da yake bayyana tsare-tsaren bikin kamun kifi a Abuja da aka saba gudanarwa a Argugun wanda aka gudanar daga 11 zuwa 14 ga Maris na 2020. Sanarwar ta ce an yi nisa da shirye-shiryen wankan sarautar da za a…
13
Aug
Daga AMINA YUSUF ALI Allah ya yi wa ɗaya daga cikin fitattun manyan Ƙasar Nijeriya, Ahmad Joda rasuwa. Ya rasu yau Juma'a, a garin Yolan Jahar Adamawa. Marigayin ya rasu ne bayan matsananciyar doguwar rashin lafiya wacce ta ƙi ci ta ƙi cinyewa. Marigayin ya rasu ne yana da shekaru 91 da haihuwa. Kuma tsohon ɗan jarida ne wanda ya yi shuhra a fagen. Haka nan, yana ɗaya daga cikin manyan Sakatarorin Gwamnatin Ƙasar nan a lokacin mulkin tsohon Shugaban Ƙasa, Janar Yakubu Gowon, yayin mulkin soja. A inda ya yi ritaya a matsayin babban sakataren ma'aikatar masana'antu. Bayan Yaƙiin…
13
Aug
Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU A wannan mako ina son hankalin mu ya karkata ne wajen nazarin yadda halayya ta gari da kyautatawa juna a mu'amala ta yau da kullum ke iya haifar da fahimtar juna da zaman lafiya a tsakanin jama'a, musammam mutane masu bambancin ƙabila, addini ko ra'ayin siyasa, da sauran harkoki da zaman tare ke iya haɗa jama'a, daga ɓangarori daban-daban. Babu shakka zaman lafiya da jama'a, tausayawa, tallafawa, da kauce wa duk wani abu da zai iya kawo saɓani da rashin fahimta a tsakanin mutane, abin a yaba ne matuƙa, babu ma kamar wannan lokaci da jama'a…
13
Aug
Daga MUSTAFA IBRAHIM ABDULLAHI ‘Yan uwa masu karatu, assalamu alaikum. Barkanmu da wannan lokaci, barkan mu da sake saduwa a wannan shafi mai ilmantarwa, da ke zayyano muku bayanai game da jikin ɗan adam, domin ku fa’idantu kuma ku ilmantu, ku san yadda jikinku ke aiki. Satin da ya gabata, mun ɗau garkuwar jikin ɗan adam domin yin bayani akai. Jikin ɗan adam mai ɗauke da ƙwayar halitta ɗai ɗai har tiriliyan ɗari, yana buƙatar dakarun tsaro na musamman masu matuƙar ƙarfi da hikima wajen kare shi daga ta'annatin ƙwayoyin cuta, waɗanda kan lahanta lafiya, har ma sukanyi kisa a…
13
Aug
Daga SADIYA GARBA YAKASAI Mai dokar bacci ya ɓuge da gyangyaɗi:Babban tashin hankalin da ya tunkaro mu iyaye wannan na kowa da kowa ne, daga iyaye maza har mata, dole kowa ya nutsu ya gane gaskiya tun lokaci bai ƙure ba. Game da harkokin biki na yaranmu, abun fa ya fara fita daga inda aka san yaran Hausawa, masoya addini. Tun daga gida muke rusa auren yaranmu. Maimakon ake shi musu albarka, yanzu ya koma tsinuwa ce take raka su ɗakin mazajensu. Wanda dai laifinmu ne iyaye mata da maza. Kowa yana da kamasho wajen jawo wa yaranmu la'antar mutane,…
13
Aug
Daga AMINA YUSUF ALI Duk da dai Hausawa sun ce: "so aljannar duniya". Haka kuma sun ce; "so gishirin rayuwa". To amma masu dabara, zaman lafiya da maslaha da dacewar halayya suka zaɓa. Matasa kada ku yaudaru da waɗancan kalamai. Duk kuwa da zaƙinsu kamar zuma sabuwa! Ku buɓe idanu da kunnuwa ku kalli gabanku. Ku guje wa yin aure don so kawai. Idan ka zaɓi dacewar halayya da tsarin rayuwa sai ka ga bayan an yi aure, soyayyar ta ginu a hankali. Ba a ce kada a yi auren soyayya ba, kuma ba a ce auren soyayya ba ya…
13
Aug
Cibiyar Yaƙi da Yaɗuwar Cututtuka ta Ƙasa (NCDC) ta bayyana ceqa an samu ƙarin mutum 753 da suka harbu da cutar korona a faɗin ƙasa a tsakanin sa'o'i ashirin da huɗu da suka gabata. Cibiyar ta bayyana hakan ne a shafinta na intanet a safiyar Juma'a, inda ta nuna ƙarin da aka samu ya shafi wasu jihohi goma sha huɗu ne. NCDC ta ce jihohin da lamarin ya sha sun haɗa da: Legas 364, Akwa Ibom 141, Oyo 74, Rivers 46, Abia 38, Ogun 24, Kwara 20, sai kuma Birnin Tarayya, Abuja mai mutum 12. Sauran jihohin su ne, Ekiti…
