15
Aug
Ƙungiyar Fulani ta Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria (MACBAN), ta yi tir da harin da aka kai wa al'ummar hanyar Rukuba da ke Jos, Jihar Filato. Haka nan, ƙungiyar ta buƙaci jami'an tsaro da su dukufa bincike don gano waɗanda suka aikata wannan mummunan aiki don su fuskanci hukunci. MACBAN ta yi waɗannan bayanan ne cikin sanarwar da ta fitar ta hannun sakatarenta na ƙasa, Baba Othman Ngelzarma, a Jos a ranar Lahadi. Ƙungiyar ta nuna damuwarta kan yaddahar yanzu ba a gano wasu mazauna yankin ba kimanin su 40 da suka ɓata sakamakon harin. Yayin da ta…
