16
Aug
Daga AMINA YUSUF ALI Gwamna Aminu Bello Masari na Jahar Katsina ya ƙaryata zargin cewa yana hararar wata kujerar mulkin bayan kammala wa'adin zangon mulkinsa na biyu a shekarar 2023. Gwamnan ya bayyana hakan ne a wajen wani taro inda ya bayyana cewa, ya riga ya yi wa mutane hidima da dama a ɓangarori daban-daban a tsawon rayuwarsa. Don haka yanzu ba zai sake neman wani muƙamin ba sai dai ya tallafi matasa 'yan baya su samu muƙamai a gwamnati. Amma sam shi ba zai ƙara neman muƙami ba, walau na gwamnati ko kuma na jam'iyya. Ya ƙara da cewa,…
