Editor

9513 Posts
INEC ta samu buƙatun rajistar zaɓe miliyan 2.4, yayin da an yi rajistar mutum miliyan 1.9 ta yanar gizo

INEC ta samu buƙatun rajistar zaɓe miliyan 2.4, yayin da an yi rajistar mutum miliyan 1.9 ta yanar gizo

Ya zuwa yanzu, Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta samu buƙatar yin rajista guda 2,449,648 daga ranar da ta fara aikin rajistar masu zaɓe (wato Continuous Voter Registration, CVR) wato 28 ga Yuni, a cewar wani jadawalin mako-mako na aikin wanda aka fitar a ranar Litinin a Abuja. Hukumar Dillancin Labarai ta Nijeriya (NAN) ta ruwaito cewa jadawalin ya kuma nuna cewa ya zuwa yanzu, 'yan Nijeriya 1,923,725 ne su ka kammala matakan farko na yin rajistar su ta hanyar yanar gizo a cikin wannan lokacin na mako bakwai a daidai ƙarfe 7 na safiyar ranar Litinin, 16 ga Agusta. Bugu…
Read More
Saudiyya za ta ƙara wa’adin yin biza ga ƙasashen da ke cikin dokar hana tafiye-tafiye

Saudiyya za ta ƙara wa’adin yin biza ga ƙasashen da ke cikin dokar hana tafiye-tafiye

Daga AMINA YUSUF ALI Ƙasar Saudiyya ta sanar da cewa ta tsawaita wa'adin yin biza ga wasu ƙasashen da suke fuskantar dokar hana tafiye-tafiye. Inda ta tsawaita wa'adin har zuwa 30 ga watan Satumban bana. Kuma an ba su wannan dama ne ba tare da an caje su ko sisi ba. Ministan hulɗa da ƙasashen waje na Saudiyya shi ya bayyana hakan a shafinsa na Tiwita. Ya ƙara a cewa, wannan dama ta tsawaita wa'adin bizar za ta yi aiki ne kawai ga mutanen da suka riga suka yi bizar shiga ƙasar ta Saudiyya amma kuma sai bizar ta su…
Read More
Abin da ya sa ba mu kashe tubabbun ‘yan ta’adda, cewar sojoji

Abin da ya sa ba mu kashe tubabbun ‘yan ta’adda, cewar sojoji

Rundunar sojan Nijeriya ta ce, babban taro na duniya wanda ita ma Nijeriya ta sanya hannu a kansa, bai yarda da kashe tubabbun 'yan ta'addan da suka miƙa wuya ba. Rundunar ta faɗi haka ne a matsayin martani ga ra'ayin wasu 'yan ƙasa da ke ganin cewa me zai hana a kashe 'yan Boko Haram ɗin da suka ce sun tuba maimakon amincewa da su su ci gaba da rayuwa a cikin al'umma. MANHAJA ta kalato cewa a tsakanin watanni ukun da suka gabata, mayaƙan Boko Haram da na ISWAP sama da 3,000 ne aka damƙe ko suka tuba suka…
Read More
Rashin tsaro: INEC ta tsaida aikin rajistar zaɓe a ƙananan hukumomi 5 a Filato

Rashin tsaro: INEC ta tsaida aikin rajistar zaɓe a ƙananan hukumomi 5 a Filato

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta dakatar da aikin rajistar masu zaɓe da ake yi a faɗin ƙasar nan a ƙananan hukumomi biyar na Jihar Filato. A wata sanarwa da Madam Caroline Okpe, Sakataren Gudanarwa ta INEC, ta fitar a madadin Kwamishinan Zaɓe mai zama a jihar (REC), a ranar Litinin a Jos, ta ce an ɗage aikin ne saboda dokar hana zirga-zirga da gwamnatin jihar ta saka. Ta ce, “Ɗage aikin zai shafi cibiyoyin rajistar a ƙananan hukumomin Barkin Ladi, Bassa, Jos ta Gabas, Jos ta Arewa da kuma Riyom har sai hali ya yi. “INEC ta na tabbatar wa da sababbin…
Read More
Tsohon mataimakin shugaban Majalisar Dattawa, Ibrahim Mantu ya kwanta dama

Tsohon mataimakin shugaban Majalisar Dattawa, Ibrahim Mantu ya kwanta dama

Allah Ya yi wa tsohon mataimakin shugaban Majalisar Dattawa, Ibrahim Nasiru Mantu. Bayanai sun nuna marigayin ya rasu ne a cikin daren Litinin a wata asibitin Abuja bayan fama da rashin lafiya. A halin rayuwarsa, marigayin cikakken ɗan siyasa ne, kuma tsohon sanata da ya wakilci Filato ta Tsakiya a Majalisar Dattawa. An zaɓe shi a matsayin sanata ne 1999 inda ya zama mataimakin shugaban Majalisar a shekarar 2000. Baya ga haka, Mantu ya yi aiki a wurare da dama tare da riƙe muƙamai daban-daban inda ya ba da tasa gudunmawa ga cigaban ƙasa. An haifi Mantu ne a ranar…
Read More
Sabon Shugaban Ƙasar Zambia, Hichilema ya caccaki tsohuwar gwamnatin Lungu

Sabon Shugaban Ƙasar Zambia, Hichilema ya caccaki tsohuwar gwamnatin Lungu

Sabon zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasar Zambia, Hakainde Hichilema, ya caccaki gwamnatin da ya gadana tare da bayyanata a matsayin gwamnatin danniya. Hichilema ya caccaki tsohuwar gwamnatin ne a lokacin da yake yi wa 'yan ƙasarsa jawabi a Litinin da ta gabata a matsayinsa na sabon zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasar. Tare da yi wa talakawansa alƙawarin samar musu da dimukuraɗiyya ingantacciya kuma mai tsabta. Da yake jawabi jim kaɗan bayan da tsohon Shugaban Ƙasar, Edgar Lungu, ya amsa shan kaye, Hichilema ya ce shi da jama'arsa sun sha baƙar wahala a tsohuwar gwamnatin ƙasar. Hichilema ya ce a matsayinsa na Shugaban Ƙasa, waɗanda…
Read More
Amincewa da tubabbun ‘yan Boko Haram na iya haifar da tawaye a Borno – Zulum

Amincewa da tubabbun ‘yan Boko Haram na iya haifar da tawaye a Borno – Zulum

Gwamnan Jihar Borno, Babagana Uamara Zulum, ya bayyana cewa tubabbun 'yan Boko Haram su 1,000 da suka miƙa wuya sun bar gwamnatin jihar da al'ummarta cikin wani mawuyacin halin tsaro mai baki biyu. A cewar gwamnan, muddin gwamnati da masu faɗa a ji a jihar ba su haɗa kai sun ɗauki matakin daƙile matsalar tsaron da jihar ke fuskanta a halin yanzu ba, hakan ka iya haifar da 'yan tawayen farar hula a jihar. Zulum ya bayyana haka ne a lokacin da yake yi wa shugabannin jami'an tsaro da sarakuna jawabi a Bama da Gwoza. Ya ci gaba da cewa,…
Read More
Buni ya jagoranci gwamnonin APC don zawarcin Rashidi Ladoja a Ibadan

Buni ya jagoranci gwamnonin APC don zawarcin Rashidi Ladoja a Ibadan

Daga AMINA YUSUF ALI A Lahadin da ta gabata gwamnonin APC guda uku suka ziyarci Ibadan, babban birnin Jihar Oyo, domin zawarcin dattijon jam'iiyyar PDP kuma tsohon gwamna, Alhaji Rashidi Ladoja, zuwa jam'iyya mai mulkin ƙasa ta APC. Gwamnonin sun yi wannan tafiya ne a ƙarƙashin jagorancin Shugaban Kwamitin Riƙo na jam'iyyar APC, Gwamna Mai Mala Buni na Jihar Yobe. Har ila yau, Gwamnonin sun ziyarci wani babban mutum na Majalisar Dattijan Yarbawa, (YCE), Dakta Kunle Olajide. Sai kuma sarkin Musulmi na Ƙasar Yarabawa, Alhaji Dawud Akintola. A tare da Mai Mala Buni akwai Gwamnan Jihar Kebbi, Atiku Bagudu da…
Read More